✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Allah Ya yi wa Shugaban Gidauniyar A.A Rano rasuwa

Za a yi sallar jana'izarsa a Fadar Sarkin Rano a safiyar ranar Juma'a.

Allah Ya yi wa Alhaji Dahiru Umar Rano, Shugaban gidauniyar fitaccen dan kasuwar man fetur a Najeriya, Auwalu Abdullahi Rano wato A.A Rano Foundation rasuwa.

Dan uwan mamacin, Muhammad Jamilu Abdullahi, ya sanar cewa ya rasu ne a daren Juma’a, yana da shekara 46.

Allah Ya yi masa cikawan ne a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano (AKTH), bayan fama da rashin lafiya.

Za a yi jana’izarsa a ranar Juma’a da misalin karfe 11 na safe a Fadar Mai Martaba Sarkin Rano, Alhaji Kabiru Muhammad Inuwa.

Kafin rasuwarsa ma’aikaci ne a Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kano, kuma yana rike da sarautar Chiroman Shamaki na Mmasarautar Rano.

Gidauniyar A.A Rano, gidauniya ce da take tallafa wa dalibai da kudin karatu, tare da biya wa marasa lafiya kudin magani ko kudin aikin tiyata.

Tana kuma tallafa wa al’umma da abinci a lokacin azumin watan Ramadan gami da sauran ayyukan jin kai a cikin jama’a.