✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Allah Ya yi wa tsohon shugaban Mali Ibrahim Boubacar Keita rasuwa

Hambararren shugaban na Mali ya rasu ne a gidansa da ke Bamako.

Allah Ya yi wa tsohon shugaban kasar Mali, Ibrahim Boubacar Keita rasuwa bayan ya shafe shekara 76 a doron kasa.

Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ya ruwaito tsohon ministan shari’ar kuma tsohon mai ba shi shawara yana cewa ya rasu ne a yau Lahadi.

Haka kuma majiyoyin labarai daga kasar ta Mali sun ce iyalan Keita sun sanar da mutuwar tasa da safiyar yau Lahadi, sai dai ba su fayyace musababbin mutuwar tasa ba.

Mahukunta sun ce hambararren shugaban na Mali ya rasu ne a gidansa da ke Bamako, babban birnin kasar.

Keita, wanda aka fi sani da IBK, ya jagoranci kasar ta yammacin Afirka daga watan Satumba na 2013 zuwa Agusta 2020, wanda wannan shekaru bakwai da ya yi a karagar mulki suna cike da tashin hankalin sakamakon masu ikirarin jihadi da suka addabi kasar.

A shekarar 2020 din ce sojoji suka yi masa juyin mulki bayan shafe watanni ana zanga-zangar kin jinin gwamnati.