✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Al’ummar Tangale ta shirya bikin cin naman kare

Za su yi kwana uku suna bikin cin naman kare da baje koli al'adu da sana'o'in al'ummar kasar Tangale

Al’ummar Tangale da ke garin Billiri a Jihar Gombe na shirye-shiryen farfado da dadaddiyar al’adarsu da suka daina ta Lo-Bai, ko Palam Tangale, inda ake cin naman kare.

Al’ummar ta ce a bana za a dauki kwana uku ana gudanar da bikin, wanda a kowace rana za a gabatar da lacca ga al’ummar kasar Tangale gami da shagulgula da kuma cin naman kare.

Kwamitin shirye-shiryen bikin ya ce masu sana’ar gargajiya a kasar Tangale kamar makera da masu magungunan gargajiya da sauransu za su baje kolin kayan gargajiyarsa da gadon gidajensu a lokacin bikin.

Kwamitin ya ce hakan zai taimakawa wajen bai wa ’yan kabilar Tangale damar yin alfahari da kuma ciyar da al’adunsu gaba, kawo hadin kai da bude ido da kuma bunkasa tattalin arzikin kasa da samar da ayyukan yi a kasar Tangale.

A cewar shugabannin kwamitin, bikin na daga cikin muhimman ranakun wasan gargajiyar Tangale da aka daina gudanarwa tsawon lokaci; Bayan an gano gibin da rashin gudanar da shi ya haifar a tsakanin yara masu tasowa, sai suka hada kai don ganin an dawo da al’adar.

“Mu masu tasowa za mu farfado da ita don karfafa al’adunmu na ganin ba mu bari al’adarmu ta mutu ba saboda daddaden tarihi da muke da shi, amma da wannan za mu fara,” inji su.

Sanarwar da Shugaban kwamitin, Jessy Mallums Mai Dukkan Tangale da Sakatarensa, Dulyamba Alkeria Bagauda, suka fitar ta ce bikin zai gudana ne a garin Billiri ranar 26 zuwa 28 na wannan wata na Disamba.

Ta ce bikin na Lo-Bai ko Palam Tangale daidai yake kuma ba shi da bambanci da na ’yan kabilar Ngas da ke Jihar Filato, wadanda su ma suke gudanar da tasu a shekara-shekara.