✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Amarya da mahaifiyarta sun mutu a hatsarin kwalekwale

Jirgin na dauke da mutum 30 yawancinsu mata a Karamar Hukumar Goronyo,Jihar Sokoto

Mutum sun mutu sakamakon nutsewar da wani kwalekwale ya yi a Kogin Birjingo na Karamar Hukumar Goronyo ta Jihar Sokoto.

Kwalekwalen na dauke da fasinjoji 30 mafi yawa mata, daga cikinsu har da wata budurwar da aka sa ranar bikinta da mahaifiyarta.

Kansila Birjingo, Isa Muhammad ya ce fasinjojin da abin ya rutsa da su ranar Laraba ma’aikatan wata gonar shinkafa ce da ke tsallaken ruwa.

Mai Garin Birjingo, Alhaji Shehu Dangaladima ya ce kwalekwalen ya nutse ne saboda mutanen da ya dauka sun yi masa yawa.

Shugaban riko na karamar hukumar, Zakari Shinaka ya ce an tura ‘yan su 50 sun tsamo wadanda ruwan ya ci da kuma ceto wasu masu rai.

“An tsamo gawarwaki 7 ana kuma ci gaba da laluben mutum 2 da suka bace”, inji shi.

Shinaka ya jajanta wa iyalan wadanda iftila’in ya afka wa, tare da kira ga sarakan ruwan yankin su kama duk jirgin da ya dauki mutane fiye da kima.

“Kar ku bar kwalekwalen da ke dauke da mutane fiye da kima ya wuce, da kuma in ana yin ruwa mai iska”, inji Shinaka

Ya kuma ba mutanen garin tabbacin za a karo musu tallafin abinci da kwale-kwale.