✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Amarya ta rasu ana kokarin kai ta gidan miji

Ta rasu sa'o'i kadan bayan daura aurenta da angonta a Kano.

Wata amarya da aka daura aurenta ta rasu a yayin da ake kokarin kai ta gidan miji a ranar daurin auren.

Amaryar, Hannatu Yahaya, wacce take zaune a unguwar Kawon Maigari a Jihar Kano ta rasu ne sa’o’i kadan bayan daura aurenta da angonta mai suna Isyaka Yusuf.

An dai daura auren Hannatu da angonta Isyaka ne a safiyar Asabar, 27 ga watan Nuwanbar 2021 a Masallacin Bulama kamar yadda ’yan uwanta suka bayyana.

Wani dan uwanta ya bayyana cewa tun bayan daurin auren nata suka lura cewa Hannatu ta shiga wani hali inda ta rika fizge-fizge da lalata abubuwan amfani.

Ya ce bayan yi mata addu’o’i ta samu sauki daga bisani aka dauke ta zuwa asibiti sai dai kafin a karasa da ita asibitin ta ce ga garinku nan.

Dama dai tun gabannin daurin auren, amarya Hannatu ta yi fama da jinyar olsa, har aka kwantar da ita a asiabiti amma daga baya ta warware.