✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Amaryar Sarkin Jama’a ta rasu a wurin haihuwa

Amaryar sarkin ta rasu ne a wurin haihuwa.

Allah Ya yi wa Hajiya Zainab Muhammad Isa, amaryar Mai Martaba Sarkin Jama’a, Alhaji Muhammad Isa Muhammad, rasuwa.

Hajiya Zainab, wacce ita ce matar Sarkin ta hudu, ta rasu ne a yayin haihuwa a ranar Litinin.

Da yake sanar da rasuwar, Sakataren Masarutar, Alhaji Yakubu Isa Muhammad (Dokajen Jama’a), ya ce ta rasu tana da shekara 32 a duniya.

An yi jana’izarta kamar yadda addinin Musulunci ya tanada a Masarautar Jama’a da ke garin Kafanchan, Jihar Kaduna.

Marigayiya Zainab, ’yar asalin Jihar Osun, wadda aka haifa a garin Kafanchan, ta auri Mai Martaba Sarkin Jama’a, Alhaji Muhammad Isa Muhammad II, ne a shekarar 2019.

Marigayiyar wadda aka hafia ranar 16 ga Nuwamba, 1989, ta yi makarantar firmare da sakandare a makarantar El-Morijah da ke garin Kafanchan, kafin daga nan ta wuce makarantar sakandaren ’yan mata da ke garin Kafanchan (GGSS), daga shekarar 2002 zuwa 2008.

Daga nan ta wuce Kwalejin Kimiyya da Kere-kere ta Jihar Filato inda ta samu shaidar Difloma a kan harkokin Kasuwanci.