✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Amaryar TikTok: Hafsa Tuge Ta Yaudari Kannywood —Biffa

Darktan fim din Amarar TikTok ya ce mage-a-kwali jarumar fim din ta yi wa kowa a masana'antar Kannywood

Daraktan fim din Amaryar Tiktok da ya tada kura a baya-bayan nan Ahmad Biffa ya ce jarumar shirin da ake dambarwa a kanta Hafsa Tuge ta yaudare su. 

Darakatan ya bayyana hakan ne a tattaunawarsa da Freedom Radio, inda ya ce duk abin da ya faru babu laifinsa a ciki, domin jarumar mage-a-kwali ta yi wa kowa.

“Ina da alaka da unguwar da take zaune kuma gidan da take ba zaman kanta take a ciki ba, gida ne na ’yan uwanta.

“Kuma ina da tabbacin in dai gidan ’yan uwanta ne ya kamata su san tana da matsalar auren da bai kamata a ce sun bari an yi wannan abun ba.

“Sai dai idan su ma din dungu ta yi musu, ba ta fada musu hakikanin abin da ke faruwa tsakaninta da mijinta ba. Tunda ba lallai sun san auren bai mutu ba,” in ji Biffa.

Ya kuma ce tun da farko don guje wa irin haka, sai da suka tuntubi ’yan uwan nata, suka kuma tabbatar musu babu matsala.

Ya ce bayan bullar bidiyon matar da ta yi ikirarin mahaifiyarta ce, sai da ya tuntubi Hafsa, amma ta kada baki ta rantse ba ta santa ba, ta kuma kara da cewa kawayenta ne da suka sanya ta a gaba suke mata haka.

Kan batun maka Kannywood a kotu da mijin Hafsa ya yi kuwa, Biffa ya ce sammacin mijin nata ne ya sa suka gano gaskiya yake fada, kuma ta yaudare su, tare da nuna takaicinsa kan yadda mutane ke kin yi wa Kannywood uzuri idan irin haka ta faru.

“Mace baliga mai hankali, ya kamata a ce ta san abin da ya kamata. Domin duk wacce aka ce tayi aure daya, biyu, har zuwa uku ta san mene ne hakkin zamantakewar aure, tunda an ce aurenta uku.

“Ka ga ba maganar kuruciya ce ta saka ta yi, ka ga yaya mutum zai kawo a ransa mai irin wannan shekaru za ta aikata irin haka.”

Biffa ya  kuma ce tun a karon farko da wani ya yi ikirarin tana da aure a shafinsu na Youtube, ya dakatar da ita daga shirin don binciken gaskiyar lamarin.

Sai da na gama idda kafin in fara fim

Sai dai a nata martanin Hafsat ta ce a iya tunainta babu aure tsakaninta da mijin ta, domin har ta yi idda ma kafin shigarta fim din.

Ta ce, “Ya yi maganar nan ne don bata min suna amma ba gaskiya ba ne ya fada.

“Domin bayan na dawo daga unguwar da na fada maka ta sa mun samu sabani, sai yake ce min oh ke dama kina tunanin kin dawo a matsayin matata, ai ba ki daga cikin tsarin matana.

“Wanna maganar a nawa tunanin, a nawa hankalin, shi ne ya ba ni tabbacin babu aure tsakanina da shi.

“Saboda abubuwan da ya yi bayan wadannan abubuwan sun tabbatar da duk wani namiji da ke da aure ba zai yi su ba.”

Sai dai kuma ta ce har yanzu batun yana gaban kotu kamar yadda ya fada, domin alkalin ya ce za ta biya shi kul’i, kuma sun jiran jin nawa ya kamata ta biya shi ne.