✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

AMASCO ya ba kungiyar kanikawa tallafi

Ana bukatar irin wannan taimako daga kungiyoyi da kamfanoni.

A kokarin da yake yi na ganin ya tallafa wa al’umma don samar da aikin yi ga matasa, Kamfanin AMASCO da ke da sarrafa bakin mai da sauran nau’o’in mai, ya ba da tallafin kayayyakin gudanar da sana’ar kanikanci ga mambobin Kungiyar Kanikawa ta Kasa (NATA), reshen Jihar Borno.

Da yake karbar kayayyakin da rarraba su ga mambobin Kungiyar NATA a Maiduguri, Gwamnan Jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum wanda Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnatin Jihar, Farfesa Isa Hussaini Marte ya wakilta ya ce, gwamnatin jihar ta yaba wa kamfanin na AMASCO dangane da wannan hobbasa da ya yi na ba da wadannan kayayyakin tallafin ga masu sana’ar kanikanci.

A cewarsa, “Hakan ya yi daidai da kudirin gwamnatinmu na abubuwa 10 da muka sa a gaba da za a cimma don ciyar da Jihar Borno gaba cikin shekara 25 da suke tafe in Allah Ya so.”

Gwamna Zulum ya kara da cewa irin wannan hobbasa da Kamfanin Mai na AMASCO ya yi zai iya taimaka wa matasan jihar wajen farfadowa daga wahalhalun da suka fada sakamakon rikicin Boko Haram da kuma cutar Kwarona suka haddasa.

Don haka, ya ce ana bukatar irin wannan taimako daga kungiyoyi da kamfanoni ganin cewa, hanya ce ta kara inganta rayuwar al’umma musamman wajen samar da ayyukan yi.

Gwamnan ya ce, gwamnatinsa ta kaddamar da wata cibiya ta farko a jihar don horar da matasa sana’ar kanikanci bayan ta ba da rancen kudi ga masu kanana da matsakaitan masana’antu kimanin mutum dubu 4,250 don magance rashin aikin yi da ya yi katutu a tsakanin al’ummar jihar wanda hakan zai sa su tafi kafada-da-kafada da zamani.

Gwamna Zulum ya ce, “Gwamnatimu gwamnati ce da tafi ba da fiffiko wajen samar da ayyukan yi da kudirin, hakan zai kara inganta harkokin tattalin arzikin jihar da al’ummarta.”

Gwamnan ya ce, suna da cikakken kudirin sake samar da wasu karin cibiyoyin horar da kanikawa don ba da dama ga jama’a don samun ayyukan yi kuma hakan kan iya fadada hanyoyin samun karin kudaden shiga don rage zaman kashe wando a tsakanin al’umma.

Tun farko a jawabi Shugaban Kungiyar NATA ta Kasa, Dokta Magaji Mohammed ya mika takardar yabo ga Gwamna Zulum kan kokarinsa na ganin an samu zaman lafiya mai dorewa a Jihar Borno, kuma ya gode wa Kamfanin AMASCO dangane da wannan kokari da ya yi na ba da tallafin kayayyakin aiki ga mambobin kungiyar tasu.

Shugaban ya kuma bayyana cewa kungiya tasu kungiya ce da ta kunshi kwararru da kuma dukkan kanikawa kanana da matsakaita da wasu masana’antu da ke ba da gudunmawarsu ga tattalin arzikin kasa inda suke da mambobi sama da miliyan shida a jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya, Abuja.

Wannan shiri na ba da tallafi ga Kungiyar NATA da Kamfanin AMASCO ya yi da hadin gwiwar uwar kungiyarsu ta kasa an shirya shi ne don ba da akwatuna 100 da suke dauke da kayayyakin aikin kanikanci wadanda aka bayar ga mambobin kungiyar 100.

Kuma nan gaba, za a sake yin haka kuma a zakulo wadanda suka cancanta su ci gajiyar shirin.

Fiye da mambobin kungiyar 70 ne daga Jihar Borno za su amfana da wani tallafi na Gwamnatin Tarayya, inda za a ba su horo na musamman, wanda za a fara nan ba da jimawa ba.

Dokta Magaji ya sanar da Gwamna Zulum cewa, Kwamitin Zartarwa na Uwar Kungiyar ta Kasa, ya shirya tsaf don ba shi lambar yabo a ranar 22 ga Janairun badi a Abuja kan rawar da yake takawa wajen kula da rayuwar al’umma, kuma sun yanke shawarar ba shi mukamin Uban Kungiyar na Kasa.