✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ambaliya da zaftarewar kasa sun kashe mutum 120 a kasar Kwango

Ambaliyar ta yi barna ne a Kinshasa, babban birnin kasar

Akalla mutum 120 ne suka mutu bayan wani mamakon ruwan sama da ya haddasa ambaliyar ruwa da zaftarewar kasa a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kwango.

Ruwan dai ya yi barnar ne a daren Talata a wasu sassan Kinshasa, babban birnin kasar mai mutane kusan miliyan 15.

Ministan Harkokin Cikin Gidan Kasar, Daniel Aselo, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na DPA cewa mutane da dama da suka jikkata an kai su asibitoci mafi kusa.

Har zuwa safiyar Laraba dai, ma’aikatan ceto sun ci gaba da neman mutanen da ake fargabar sun makale a cikin baraguzan gine-ginen.

Shugaban Kasar ta Kwango, Felix Tshisekedi, wanda yanzu haka ke halartar taron Shugabannin Kasashen Afirka da Amurka a birnin Washington D.C, ya bukaci Majalisar Zartarwarsa da ta yi duk mai yiwuwa don takaita barnar.

Shugaban ya kuma ayyana kwana uku domin yin jimamin da zaman makoki, kuma ana hasashen zai takaita zamansa a Amurkan domin ya dawo kasar a kan lokaci.

A cewar kungiyar bayar da agaji ta Red Cross, ruwan mai karfin gaske ya rusa ilahirin gidajen da ke yankunan Mont-Ngafula da Ngaliema a birnin na Kinshasa.

Kazalika, ruwan ya mamaye hanyoyi da dama a kasar, ciki har da babbar hanyar kasuwancin da ake bi don zuwa Angola. (NAN)