✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ambaliya: Gwamnati ta gargadi ’yan Najeriya da su kwana cikin shiri

Kananan Hukumomi 121 daga Jihohi 27 da kuma Abuja na cikin barazana.

Hukumar Kula da Yanayi da Ayyukan Ruwa ta Kasa (NIHSA), ta yi hasashen cewa za a samu a mummunar ambaliyar ruwa a Najeriya tun daga karshen watan Agusta mai kamawa har zuwa farkon watan Oktoba.

Babban Darakta na Hukumar, Engr. Nze Clement Onyeaso ne ya bayyana hakan yayin ganawarsa da manema labarai ranar Laraba a birnin Abuja.

Ya bayyana cewa, dukkanin yankunan da aka tabbatar da ambaliyar za ta auku a bana, akwai yiwuwar za su fara fuskantar wannan yanayi a karshe-karshen watan Agusta.

NIHSA wacce ke karkashin Ma’aikatar Ruwa ta Kasa, ta ce ambaliyar za ta fi muni a wasu jahohin har da ma babban birnin tarayyya, Abuja, a tsakanin wannan lokaci da ta yi hasashe.

A cewarta, duba da hasashen da ta yi a baya, Jihohin Legas, Nasarawa, Anambra, Abiya,  Kwara, Kaduna, Ribas, Enugu, Borno da kuma Ondo, tabbas za su fuskanci matsananciyar ambaliyar ruwa a sakamakon mamakon ruwa sama wanda ya ci karo da rashin ingantattun magudanan ruwa.

“Najeriya dai tana zaune a yankin babban Kogin Neja wanda ya hada da kasashe ciki har da Kamaru, Chadi, Kwadde-buwa, Gini-bisau, Mali, da Nijar.

“Najeriya tana zaune ne a yanki na kwari fiye da sauran kasashen saboda haka da zarar kasashen  da ke kan tudu ambaliyar ta cimmusu to lallai ita ma ta shirya fuskantar irin wannan mummunan yanayi.

“Mafi akasari lokacin wadancan kasashe ke fuskantar ambaliyar shi ne watan Agusta da Satumba na kowacce shekara,” a cewar babban Daraktan.

Ya kara da cewa, hukumar tana ci gaba da kula da duk wani lamari da yake gudana wanda ya shafi ambaliyar ruwa domin tanadin matakan da suka dace.

Kazalika, ya ce za su gaba da da Ido akan hukumomin kasar Kamaru game da abinda ya shafi anbaliyar ruwa na kasar.

Engr. Nze ya kuma gargadi mazauna Jihar Legas a kan yawan haka ramuka da kuma yunkurin janyo ruwa daga babban teku domin gina abinda suke kira kayatattun birane irinsu Lekki da Banana Island, yana mai cewa hakan na iya zama barazana a nan gaba.

A cikin shirin da aka yi na hasashen yiwuwar aukuwar ambaliyar ruwa, Babban Darakta ya yi kira ga ’yan Najeriya musamman gwamnoni da su yi tanadin kyakkyawan shiri, ta hanyar tsaftace magudanan ruwa, da kuma kawar da duk wata kazanta da ka iya toshe hanyoyin ruwa.

Aminiya ta ruwaito cewa, a kwanan baya ne Hukumar NIHSA ta yi hasashen cewa Kananan Hukumomi 121 daga cikin Jihohi 27 da kuma Abuja ka iya fuskantar mummunar ambaliyar ruwa a bana.