✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ambaliya: Gwamnatin Tarayya Ta Tallafa wa Manoma 200 A Gombe

Gwamnatin ta tallafawa manoman irin don ci gaba da ayyukan noma a jihar.

A kokarin Gwamnatin Tarayya na ganin ta tallafa wa manoman da suka tafka asara a ambaliyar 2022, Ma’aikatar Aikin Gona ta Tarayya (FMARD) ta raba wa manoma 200 da iftila’in ya shafa iri mai inganci a Jihar  Gombe.

Mataimakin Darakta mai kula da tsirrai a Ma’aikatar Mista Lord Banjou, ne ya bayyana hakan a lokacin da suka kaddamar da rabon irin a Gombe.

Mista Bonjou wanda ya samu wakilcin babban jami’i mai kula da ayyuka na ma’aikatar, Mista Temile, ya ce tallafin an yi shi ne domin rage wa manoman radadin asarar da suka yi a ambaliyar.

Banjou ya kara da cewa ambaliyar ta tafi kowacce muni a tarihin Najeriya inda ta jawo hauhawar farashin abinci da kuma karancinsa, wanda idan ba a yi sa’a ba za a samu matsalar cutar Tamowa.

“Shi ya sa ma’aikatar ta samar da iri mai jure fari da kuma nuna da wuri don rabawa manoman dan rage wa musu takaicin barnar da ambaliyar ta yi musu” inji shi

A nasa jawabi Daraktan Ma’aikatar a Jihar Gombe, Dokta Musa Inuwa, wanda ya hori wadanda suka ci gajiyar ne da cewa su tabbata sun yi amfani da irin yadda ya dace.

Ya ce hakan zai taimaka musu wajen rage asarar da ta same su kuma zai bude musu wani sabon shafi na girbi mai kyau da ba zai haifar da karancin abinci ba.

Sannan ya jan hanaklinsu da cewa su tabbatar irin da aka ba su za su ririta shi yadda ya dace.

Abubuwan da aka raba wa manoman sun hada da pakitin tumatir guda 40 na albasa 20 da soborodo 20 sauran nau’ukan irin shuka.