Daily Trust Aminiya - Ambaliya: Mutum 15 sun mutu a jihar Kebbi
Subscribe

Ambaliya: Mutum 15 sun mutu a jihar Kebbi

Kididdigar da Kungiyar bayar da agaji a Najeriya ActionAid ta gudanar, ta nuna cewa ambaliyar ruwa ta salwantar da rayukan mutane 15 yayin da raunata mutum 30 gami da raba mutane 5,200 da mahallansu yayin aukuwarta cikin watanni biyu a jihar Kebbi.

Shugaban Kungiyar na Najeriya, Eni Obi, ya sanar da hakan yayin zanta wa da manema labarai a ranar Juma’a a Birnin Kebbi.

Yana cewa kididdigar da Kungiyar ta gudanar ta nuna cewa ambaliyar ruwa ta shafi mutum 11,356 a jihar Kebbi da ke Arewa Maso Yammacin Kasar.

Obi ya alakanta aukuwar ambaliyar da saukar ruwan sama mai karfi da ake samu a daminar bana wanda ya yi sanadiyar cika da tumbatsar madatsun ruwa na Bakolari da Goronyo da ke Jihar Zamfara da Sakkwato.

Ya kara da cewa ambaliyar ta lalata gonaki da amfanin gona wanda ba san adadinsu ba.

More Stories