✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ambaliya: Mutum 51 sun mutu, gidaje 4,500 sun rushe a Philippines

Gidaje sama da 4,500 sun salwanta, gonaki sun lalace.

Adadin wadanda suka mutu sakamakon ambaliyar ruwa a kasar Philippines ya haura 51, yayin da hukumomin agaji ke ci gaba da raba wa mutane abinci.

Hukumomin kasar na ci gaba da aikin ceto, inda suka kasa gano mutum 19 da ake zargin sun bace ne tun bayan afkuwar ambaliyar a ranar Kirsimeti.

Sama da mutum 270,000 ne suke neman agaji bayan afkuwar ambaliyar a tsakanin mazauna kauyukan kasar.

Ambaliyar ta yi sanadin rushewar gidaje sama da 4,500, yayin da gonaki da girmansu ya kai hekta 7,000 ruwan ya share su tare sa amfanin gonar da ke ciki.

A maimakon jama’ar kasar su yi murnarn bikin Kirismeti sun bige da aikin ceto gidajensu da dukiyoyinsu.

Lamarin ya fi munana a yankin Misamis Occidental, da ke Kudancin Tsibirin Mindanao da ke kasar.

Philippines na daga ciki kasashen da aka yi hasashen za su fi fuskantar matsala sakamakon sauyin yanayi da duniya ke fuskanta.