✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Sakamakwon Zaben Gwamnonin Najeriya Na 2023 (Alkaluma Daga:INEC)

Ambaliya: NEMA ta bai wa asibiti 4 tallafin magunguna a Kano

NEMA ta bayar da tallafin ne don taimaka wa wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a jihar.

Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) ta raba magunguna ga wasu asibitoci hudu a Jihar Kano, don tallafa wa wadanda ambaliyar ruwa ta shafa.

Da yake gabatar da kayayyakin, Babban Daraktan NEMA, Mustapha Habib Ahmed, ya ce kungiyar Map International ce ta bayar da tallafin ga asibitocin na Kano.

Ahmed, wanda ya samu wakilcin kodinetan NEMA na shiyyar Kano da Jigawa, Dokta Nuraddeen Abdullahi, ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta kara kaimi wajen samar da ingantaccen kiwon lafiya ga wadanda ambaliyar ruwa, garkuwa da mutane da ’yan fashi suka shafa.

Ya lissafa asibitocin da suka amfana da suka hada da Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad da Babban Asibitin Bichi da Babban Asibitin Wudil da kuma Babban Asibitin Karaye.

Wasu daga cikin kayan da aka bai wa asibitocin sun hadar da magunguna, kayan aiki, sirinji da dai sauransu.

A nasa jawabin, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ya gode wa hukumar kan tallafin, ya kuma bukaci wadanda suka ci gajiyar su da su tabbatar da sun yi amfani da kayayyakin yadda ya dace.

Ganduje wanda ya samu wakilcin Sakataren Zartarwa na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Kano (SEMA), Dokta Saleh Jili, ya yi kira da a ci gaba da samun hadin guiwa tsakanin SEMA da NEMA don ciyar da jama’a gaba.

Ya shawarci jama’a musamman mata masu amfani da icen girki da tukunyar iskar gas da gawayi da su rika kula da wuta da kuma kashe na’urorin lantarki a duk lokacin da ba a amfani da su.

Ya kuma yi kira ga al’ummar jihar da su daina zubar da shara barkatai a ko’ina, sannan kuma su rika share magudanun ruwa domin kauce wa ambaliyar ruwa.

Da yake mayar da martani, Daraktan Hukumar Kula da Asibitoci na Jihar Kano, Dokta Nasiru Alhassan Kabo, ya yaba wa NEMA bisa wannan karamci da ta yi wa jihar.

Kabo wanda Mataimakin Daraktan Hukumar Kula da Asibitoci, Ibrahim Abdullahi ya wakilta, ya ce asibitocin za su tabbatar da amfani da kayan aikin yadda ya kamata.