✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Ambaliya ta hallaka mutum 25 a Bauchi’

Ambaliya ta kashe mutum 25, wasu 20 kuma suka samu munanan raunuka a kananan hukumomi 15 na jihar Bauchi a bana. Gwamna Bala Mohammed ya…

Ambaliya ta kashe mutum 25, wasu 20 kuma suka samu munanan raunuka a kananan hukumomi 15 na jihar Bauchi a bana.

Gwamna Bala Mohammed ya ce gidaje 3,500 ne ruwa ya rusa, sai gonaki 2,200 da aka kiyasta hasarar za ta haura Naira miliyan 950.

Gwamnan ya bayyana haka ne lokacin da yake tarbar Darakta Janar na Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA), Air Vice Marshal Muhammad Mohammed, a Bauchi.

Gwamnan wanda mataimakinsa, Sanata Baba Tela ya wakilta ya bayyana fargaba kan karancin abinci da za a iya samu a jihar sakamakon ambaliyar.

Ya ce shi da mataimakinsa sun je kanana hukumomi takwas daga cikin wadanda ambaliyar ta shafa.

“Idan ka wuce Darazo ruwa ya ci rabin titi, idan muka sake samun ambaliya za ta iya tafiya da sauran titin.

“Idan ka je Shira kafin ka shiga Disina akwai wajen da ake kira Bakatma, za ka ga mutane suna iyo a ruwa da ya malala a kan tituna, ya yanke hanyoyin wajen baki daya”, inji gwamnan.

Ya gode wa NEMA saboda tallafin da take ba jihohi sannan ya roki Gwamnatin Tarayya ta kara agaza wa jihohi wajen magance matsalar ambaliya.

Shugaban NEMA ya ce ya je Jihar Bauchi ne don  ya fadakar da al’umma saboda matsalar ambaliyar, sannan ya jajanta ga wadanda suka rasa rayukansu ko asara.

Daraktan, wanda babban jami’i a hukumar, Bashir Gargar, ya wakilta ya koka kan yadda ambaliya ke barazana ga rayuka, kuma Jihar Bauchi na daga cikin jihohin da ake noma abinci amma tana fama da ambaliya.