✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ambaliya ta karya gadar da ta hada Arewaci da Kudancin Najeriya a Nasarawa

Ruwan sama kamar da bakin kwarya a jihar Nasarawa, ya haifar da ambaliyar da ta yi sandiyar karyewar gadar da ta hada Arewacin Najeriya da…

Ruwan sama kamar da bakin kwarya a jihar Nasarawa, ya haifar da ambaliyar da ta yi sandiyar karyewar gadar da ta hada Arewacin Najeriya da Kudancin kasar ta bangaren jihar.

Wannan dai na zuwa ne kasa da kwana biyu bayan karyewar gadar babban titin da ke kusa da Kwalejin Fasasha da ke Lafiya, babban birnin jihar.

Har wa yau, gadar Akwanga da ta karye a yanzu kuma, ita ce wacce masu ababen hawa ke amafani da ita wajen tsallakawa jihohin Kaduna da Filato da Bauchi da Gombe da Abuja.

Wakilinmu da ya ziyarci wajen da lamarin ya auku, ya ce dole ta sanya masu ababen hawa komawa bi ta kananan tituna.

Wani direban mota mai suna Ibrahim Danjuma ya ce idan har gwamnati ta gaza gyaran gadar, to babu shakka za a sha wahala, domin ita ce kadai hanyar da za a bi a tsallaka makwabtan jihohi.

“Idan ba a dau matakin gaggawa ba, to ba shakka ‘yan fashi da sauran bata-gari za su yi amfani da damar su dinga yi wa mutane sata.

“Ina rokon gwamnati da ta hada hannu da Hukumar Kula da Gyaran Tituna ta Kasa (FERMA), domin gyara gadar,” inji shi.

Duk wani yunkurin ji ta bakin Shugaban Karamar Hukumar Akwanga, Safiyanu Isa, ya ci tura, domin wayarsa na kashe har zuwa lokacin hada wannan rahoton.

Sai dai Dagacin Akwanga, Anthony Yamusa, ya ce karyewar gadar zai sanya hanyar komawa tarkon mutuwa, tare da kira ga hukumar FERMA da ta gyara ta cikin gaggawa.

“Abun damuwa ne a ce gadar da ta sada Arewacin Najeriya da Kudancin Najeriya ta karye.

“Wannan ba iya mu kadai zai shafa ba, har da tattalin arzikin Najeriya,” inji Dagacin.