✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ambaliya ta raba mutum 14,000 da gidajensu a Kebbi

Kashi 70 na mazauna yankunan kusa da kogunan Rima da Neja sun rasa muhallansu

Akalla mutum 14,000 ne suka rasa muhallansu sakamakon ambaliyar ruwa a Jihar Kebbi kawo yanzu.

Hukumar Ba da Agaji ta Jihar Kebbi (SEMA) ta sanar da haka, a lokacin da Ma’aikatar Jinkai da ba da Agaji ta Tarayya ta kaddamar da rabon tallafin COVID-19 a Birnin Kebbi, hedikwatar Jihar.

“Akwai akalla mutum 14,000 da ke gudun hijira a Jihar da yanzu haka an tsugunar a sansanonin ’yan gudun hijira da ke Gwandu, Dabai da kuma Shanga”, inji Shugaban Hukumar, Alhaji Sani Dododo.

Ya ce sama da kashi 70 na mazauna yankunan da ke makwabtaka da Kogin Rima da na Neja sun rasa muhallansu sakamakon ambaliyar da kogunan suka yi.

Sani Dododo ya kara da cewa ambaliyar da aka samu a daminar bana ta fi wadanda aka saba gani a baya a Jihar.

Buhari zai ba da tallafi –Minista

A jawabinta, Ministar ma’aikatar, Sadiya Umar Faruk, ta bayyan ambaliyar da ta lalata amfanin gona da sauran kadarori a jihar a matsayin babbar iftila’in da ya samu Najeriya a shekarar 2020.

Sadiya, wadda ta yi zagaye domin ganin irin asarar da ambaliyar ta haddasa, ta ce Shugaba Buhari ya umarci ma’aikatarta da ta tattara bayanan wadanda abun ya shafa domin Gwamnatin Tarayya ta kawo musu dauki.

Ta ce Shugaban ya damu matuka kan amfanin gonar da aka yi asara, musamma ta shinkafa a Jihar Kebbi.

Don haka ta ce zai yi dukkannin mai yiwuwa domin ganin ba a samu tasgaro a harkar noman shinkafa ba.