✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ambaliya ta sa ’yan majalisar Kogi hijira daga gidajensu

Ambaliya ta mamaye unguwar 'yan Majalisar Dokokin Jihar Kogi tare da tilasta musu hijira.

Ambaliya ta mamaye ilahirin unguwar ’yan Majalisar Dokoki ta Jihar Kogi tare da tilasta wasunsu yin kaura.

Ambaliya da aka samu a Jihar ta mamaye wasu manyan hanyoyin, lamarin da ya hana yiwuwar tafiye-tafiye zuwa wasu sassan jihar.

Unguwar da ke kan hanyar kauyen Ganaja na dauke da gidajen ’yan majalisa guda 26, in banda yanzu da ambaliyar ta tilasta wa mazaunanta yin kaura.

Rahotanni sun ce zuwa ranar Lahadi, ba a iya zuwa kauyen na Ganaja dole sai an yi amfani da kwalekwale.

Hakan ya tilasta wa matafiya sauya hanya domin zuwa Lokoja, babban birnin jihar.

Akalla gidajen ’yan majalisa takwas ne ba za su shigu ba sakamakon iftila’in.

Dukkannin yunkurin jin ta bakin ’yan majalisar ya ci tura saboda dukkanninsu sun ki cewa uffan.