Ambaliya ta yi ajalin mutum 7, ta rusa gidaje 74,713 a Adamawa | Aminiya

Ambaliya ta yi ajalin mutum 7, ta rusa gidaje 74,713 a Adamawa

Ambaliyar Ruwa
Ambaliyar Ruwa
    Abubakar Muhammad Usman

Ambaliyar ruwa ta yi ajalin mutum bakwai tare da rusa gidaje 74,713 cikin wannan wata na Agusta a fadin jihar.

Hukumar Bayar Da Agajin Gaggawa ta Jihar Adamawa (ADSEMA),ce ta bayyana hakan ga Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa NAN a ranar Alhamis.

Cikin sanarwar da ya fitar a birnin Yola, Sakataren ADSEMA, Dokta Mohammed Sulaiman, ya ce ambaliyar ta shafi kauyuka 79 da ke Kananan Hukumomi 16 da ke jihar.

Ya ce daga cikin Kananan Hukumomin da ambaliyar ta fi shafa sun hadar da Demsa, Yola ta Kudu, Lamurde, Yola ta Arewa da kuma Girei.

“Tun daga 11 ga watan Agusta zuwa yanzu, ambaliyar ta shafi mutum 74,713 a yankuna 79 na Kananan Hukumomi 16 da ke fadin jihar nan.

“Karamar Hukumar Demsa na daga cikin inda lamarin ya fi tsananta, inda ambaliyar ta shafi mutum 8,332 daga yankuna tara, yayin da kuma mutum daya ya mutu.

“Karamar Hukumar Lamurde na da mutum 7,725 daga yankuna takwas da lamarin ya shafa.

“Sai Yola ta Kudu da Yola ta Arewa, inda mutum 7,551 da 6,235 lamarin ya shafa.

“Mutum biyu sun rasu a Karamar Hukumar Maiha, sannan Shellen, Numan, Girei da Madagali an samu kowane mutum daya ya mutu,” cewar Sulaiman.

Ragowar yankunan da ambaliyar ta shafa sun hadar da Fufore wadda mutum 4,875 daga yankuna 11 abun ya shafa, yayin da kuma Song ke da mutum 5,359 su ma daga yankuna uku ya shafa.

Dokta Mohammed Sulaiman ya kuma roki Gwamnatin Tarayya da sauran hukumomin bayar da agaji da su tallafa wa wanda ambaliyar ta shafa.