Ambaliya Ta Tafi Da Hanyar Jirgin Kasa Daga Legas Zuwa Kano | Aminiya

Ambaliya Ta Tafi Da Hanyar Jirgin Kasa Daga Legas Zuwa Kano

Titin jirgin kasa. (Hoto: adobestock)
Titin jirgin kasa. (Hoto: adobestock)
    Halima Djimrao da Muhammad Auwal Suleiman


Ruwan sama ya lalata hanyar jirgin kasa a kudu maso yammacin Najeriya, lamarin da ya tilasta jinkirta farfado da zirga-zirgar jirgin kasa daga Legas zuwa Kano. 

A da dai da yammacin ranar Juma’a aka shirya dawowar zirga-zirgar.

Shirin Najeriya a Yau ya duba wannan lamari da ma muhimamncin dawo da sufurin jiragen kasar ga al’ummar Najeriya.