✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ambaliyar Jigawa: Sufurin kwale-kwale ba bisa ka’ida ba na kara cin rayuka

Baya ga haka kuma kamar jihohi da dama, ta lalata madatsun ruwa da gadoji da hanyoyi da dama.

Tun bayan da aka fara ruwan sama kamar da bakin kwarya a watan Agusta, ambaliyar ta raba dubban mutane da muhallansu tare da halaka sama da wasu 100 a fadin jihar Jigawa.

Baya ga haka kuma kamar jihohi da dama, ta lalata madatsun ruwa da gadoji da hanyoyi da dama.

Premium Times ta rawaito wani mai suna Surajo Ya’u a Karamar Hukumar Ringim na cewa a sanadiyyar kifewar jirgin ruwa ya rasa matarsa da dansa, har ma da surikarsa.

“Na rasa matata Nasiba, da surukata Suwaiba, da dana Mahmud a kan hanyarsu ta zuwa garin Siyango gaisuwar mutuwa,” in ji shi.

Ita ma wata mai suna Rabi Hassan ta ce ambaliyar ta sanya ta rasa gidanta da dabbobi.

Ta ce, “Sai komawa sansanonin ’yan gudun hijira na yi da zama, na shimfida zanina na kwanta da dare, na kuma lulluba da hijabina.”

A hannu guda Mai Unguwar Majiyawa ya ce ambaliyar ta shafe akalla gonaki 300 a yankin.

“Komawa makarantar firamare muka yi har sai da ruwan ya ja baya.

“Sai dai mun samu tallafi daga wani bawan Allah, amma muna bukatar kari daga gwamnatin jihar”, inji shi.

Masu kwale-kwale na cin karensu babu babbaka

Wani mai suna Hussaini ya ce yakan samu akalla Naira 3,000 zuwa N5,000 a rana idan ya tsallaka da fasinjojin da ke zuwa inda Gadar Birnin Kudu take a baya kafin ambaliya ta karya ta.

“Muna iya bakin kokarinmu don taimaka wa mutane. Da babu mu, da lamarin ya fi haka ta’azzara.

“’Yan jarida ne kawai ke zuwa nan, sai ’yan sanda da suka taba zuwa sau daya suka kama ni da wasu saboda kwale-kwalenmu da ya taba kifewa.

“Mun samu akalla gawarwaki 20 a yankin nan sakamakon hatsarin kwale-kwalen

“Wasu mun mika su kauyuka, wasu kuma muka binne su bayan daukar lokaci ba a zo neman su ba.

Haka zalika ya ce suna karbar kudi kadan ne ga fasinjojinsu da suka fito daga Birnin Kudu domin kai ’yan uwansu asibiti, amma ba sa karbar ko kwandala daga tsofaffi, ko wadanda suka dauko gawa.

“Muna karbar Naira 50 ne idan muka dauko muatne 12 a jirgi, amma idan ruwan ya taru sosai biyar muke dauka mu kara kudin cike gurbi.

Shi ma dai wani mai suna Ya’u Musa da ke daukar mutane a kwale-kwalen ya ce a da yana zirga-zirgarsa ne a Legas da ke Kudancin Njaeriya, sai dai zuwansa Jigawa ya watsar da dabi’ar ba da rigar ceto a ruwa.

“A Legas, idan aka ba jirgin ruwa rigunan guda biyar, to mutum biyar kawai ke da izinin shiga jirgin, babu damar yin lodi fiye da kima, amma nan duk ba ruwansu da wannan”, in ji shi.