✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ambaliyar ruwa ta kara barna a Kebbi

Ambaliyar ruwa ta kara barnata dimbin dukiya a garin Argungu Karamar Hukumar Argungu, Jihar Kebbi. Ambaliyar ta rusa gidaje da dama ta kuma tafi da…

Ambaliyar ruwa ta kara barnata dimbin dukiya a garin Argungu Karamar Hukumar Argungu, Jihar Kebbi.

Ambaliyar ta rusa gidaje da dama ta kuma tafi da dabbobi da har yanzu ba san dadinsu ba.

Malam Mansur Makama Argungu a zantawarsa da wakilinmu ya ce ruwan sama ne da aka yi da misalin 12 daren Lahadi ya yi ambaliya a cikin gari da kauyukan Argungu.

Mazaunin na garin, ya ce an tsinci gawar dabbobi da suka mutu a ambaliyar, baya ga wadanda ta yi awon gaba da su.

Yankunan da ambaliyar ta shafa a cewarsa sun hada da, Gwazange da Bakin Kasuwa da Gargar Iddi da Bayawa da Garkar Dogo Kafi Mari.

Ya ce jagorori a Karamar Hukumar sun jajanta wa mutanen ciki har sanannen malamin addini na Kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Ikamatis Sunnah, Shaikh Abubakar Giro Argungu.