✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ambaliyar ruwa ta kashe mutane 22 a Iran

Ambaliyar ruwa kan mamaye gidaje a duk lokacin da aka yi mamakon ruwan sama.

Ambaliyar ruwa ta hallaka akalla mutane 22 a Kudancin kasar Iran.

Shugaban kungiyar bayar da agaji ta Red Cross a yankin Estahbah, Hossein Darvishi, ya ce akwai karin wasu mutane da ba a ji duriyarsu ba tun bayan da ambaliyar ruwan ta afku.

A yayin da suke tabbatar da faruwar ifti’alin a ranar Asabar, hukumomin yankin sun ce tsakiyar lardin Estahbah ne ambaliyar ta fi yi wa ta’adi.

Kamfanin Dillancin Labarai na IRNA ya ruwaito Gwamnan Estahban, Yousef Kargar yana cewa, ruwan sama kamar da bakin kwarya da ya sauka a ranar Juma’a a tsakiyar lardin Estahban ya haifar da ambaliya.

Wasu hotunan bidiyo da aka yada a kafafen sada zumunta na cikin gida da na waje sun nuna yadda wasu motocin suka tsamo-tsamo tamkar leda a cikin ruwa yayin da iyaye ke kokarin ceto ’ya’yansu daga motocin.

Khalil Abdollahi, shugaban sashen kula da rikice-rikicen lardin, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters cewa akalla mutane 55 ne aka ceto a ambaliyar, wadda ta dilmiyar da motoci 15.

A shekara ta 2019, ambaliyar ruwa irin wannan ta yi ajalin mutum 76 a Kudancin Iran sannan ta haddasa wa magidanta asarar da ta kai darajar kudi Dala miliyan 2000.

Kasar Iran na cikin kasashen da ke fuskantar karancin ruwan sama, lamarin da ke haifar da mummunan fari.

Amma kuma lokaci zuwa lokaci, ambaliyar ruwa kan mamaye gidaje a duk lokacin da aka yi mamakon ruwan sama.