✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ambaliyar ruwa ta kashe mutum 27 a Malaysia

Ana fargabar samun karuwar mutanen da suka rasu yayin da ake ci gaba da gano gawarwaki.

Kawo yanzu gawawwakin mutum 27 aka samu da ajali ya katse musu hanzari sakamakon ambaliyar ruwa da auku a Malaysia biyo bayan mamakon ruwan saman da ya sauka a kasar a kwanakin nan.

Ambaliyar wadda mahukunta suka bayyana cewa ita ce mafi muni da aka gani a kasar a shekarun bayan nan, ta janyo mutum fiye da dubu 70 sun rasa muhallansu.

Mamakon ruwan saman da ya kwashe kwanaki uku yana sauka ne ya janyo mummunar ambaliyar ruwan a jihohi shida na kasar wadda ta ci wurare fiye da 200 ciki har birane da kauyuka.

Rahotanni sun ce jiragen soji ne suka rika aikin raba abinci ga daruruwan mutanen da suka makale a gidajensu wadanda karfin ruwan ya hana jami’an agaji kai musu dauki.

Jihar Selango wadda ta fi kowacce arziki da ke gab da Kuala Lumpur, babban birnin Malaysia na jerin yankunan da ambaliyar ta fi yi wa barna.

Wani mutum yana tsinto kayayyakin gidansa a birnin Shah Alam bayan da ambaliyar ta rutsa da shi.
Hoto: AFP

A birane kamar Shah Alam, har ya zuwa ranar Talata ruwan saman mai karfin gaske na ci gaba dauka wanda ya tsayar da duk wata hada-hada.

Lamarin dai ya fusata yan kasar da suka ganin cewa hukumomin gwamnati ba su dauki matakan gargadi ko kuma aika tallafi wajen kwashe mutanen da suka makale a wuraren da ambaliyar ta ratsa.

Har ya zuwa ranar Laraba ana fargabar cewa za a samu karuwar mutanen da suka rasu yayin da ake ci gaba da gano gawarwaki.

Hukumar Hasashen Yanayi ta kasar ta ce akwai yiwuwar za a fuskanci karin tsawa da ruwan sama mai karfi a jihohin Selangor da Pahang a ranar Laraba.