✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ambaliyar ruwa ta kashe mutum 5 a Indiya

Gidaje da dama sun rushe a sanadin ambaliyar ruwan.

Akalla mutum biyar sun mutu yayin da fiye 30 suka bace a sakamakon wata ambaliyar ruwa da ta auku safiyar Laraba a Arewacin Kasar Indiya.

Wannan ya faru ne sakamakon mamakon ruwan sama da aka tashi da shi a wasu sassan kauyukan da ke nesa da Jammu a yankin Kashmir na kasar.

  1. Lambar NIN: Za a yi wa ’yan Najeriya da ke Amurka rajista
  2. Kotu ta sa a ci gaba da tsare Abduljabbar a gidan yari

An gano gawar mutum biyar kawo yanzu kuma kusan mutane 36 sun bace daga kauyen Honjar Dacchan, kamar yadda jami’in ’yan sanda na gundumar Kishtwar, Shafqat Bhat ya bayyana.

Gine-gine da dama sun salwanta sakamakon ambaliyar da ta afku, kamar yadda tashar labarai ta NDTV ta rawaito.

Bhat ya ce ana ci gaba da kokarin lalubo wadanda suka bace.

Duba da hasashen samun ruwan sama mai yawa, hukumomin gundumar sun roki mutanen da ke zaune kusa da gabar ruwa da kuma wuraren da ke da matsalar zaizayar kasa da su kasance masu lura.

Ofishin kula da yanayi na yankin Srinagar ya ba da shawara tare da gargadi game da yawaitar ruwan sama wanda zai iya haifar da ambaliyar ruwa, zaftarewa da zaizayar kasa, musamman a gundumar Jammu da ke yankin Kashmir.

Zaftarewar kasa da ambaliyar ruwa sun zama ruwan dare a lokacin damuna a kasar Indiya, wanda ke farawa daga watan Yuni zuwa Oktoba na kowace shekara.

Ruwan sama yana da muhimmanci ga harkar noma amma galibi yakan haifar da mummunar asara ga dukiya da albarkatun gona, wanda ke haifar da asarar daruruwan rayuka.