✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ambaliyar ta lalata gonaki 14,496 a Kano —NEMA

Ibtila'in ya lalata gonaki 5,775 a Karamar Hukumar Dawakin Kudu, 1,405 a Bebeji, 260 a Rano.

Hukumar ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) ta ce ambaliyar ruwa ta lalata gonaki akalla 14,496 da ke kananan hukumomi biyar na jihar Kano.

Babban Daraktan Hukumar, Mustapha Ahmed-Habib ne ya bayyana hakan ranar Talata, yayin rangadin tattaro rahoton barnar da ambaliyar ta yi a kananan hukumomin Warawa da Wudil.

Ya ce ibtila’in ya lalata gonaki 5,775 a Karamar Hukumar Dawakin Kudu, da 1,405 a Bebeji, sai 260 a Rano.

Ya ce Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bai umarnic hukumar ta tantance barnar da ambaliyar ta yi, domin tallafa wa wadanda lamarin ya shafa.

“Mun zo rangadin tantance barnar Ambaliya a garuruwan Wudil da Gishiri Wuya da Larabar Gadon-Sarki, amma yanayin hanyar ya hana mu karasawa —Ba za mu iya hayewa ba, saboda motocinmu duk sun makale a ruwa da tabo.

“Duk da haka za mu cigaba da rangadin tantancewar a duk inda ambaliyar ta shafa a Najeriya,” in ji shi.

Mustapha ya ce za su mika rahoton ga Ma’aikatar Jin Kai da Kula da Bala’o’i, tare da alkawarin gwamnati za ta tallafa wa wadanda ambaliyar ta shafa, don rage asara.

A nasa jawabin, Babban Sakataren Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Jihar Kano (SEMA), Saleh Jili, ya alakanta ambaliyar da fitar ruwa mai yawa daga madatsar ruwa ta Tiga.

Daya daga cikin wadanda abin ya shafa, Malam Nasiru Qayya, ya bukaci gwamnatin da ta gyara musu titin Ladi Makole zuwa Larabar Gadon-Sarki, wacce ambaliya ta lalata, domin samun saukin shige da fice.