✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ambaliyar ruwa ta raba mutum 300 da gidajensu

Gidaje 100 ne suka rushe sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya da ya kai awa tara ana yi a jihar Anambra. Akalla mutum 300…

Gidaje 100 ne suka rushe sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya da ya kai awa tara ana yi a jihar Anambra.

Akalla mutum 300 ne ambaliya ta tilasta wa barin gidajensu sakamakon ruwan a yankin Eket, inda mazauna suka ce galibin gidajensu sun cika da ruwa saboda rashin kyan magudanan ruwa.

“Ina cikin gidana kawai sai na ga ruwa ya fara shigowa da karfi. Na yi asarar kusan duk abun da na mallaka”, inji Ubong Mark, mazaunin unguwar.

Yankin Eket ya shafe sama da shekara takwas yana fama da ambaliyar ruwa.

Mazauna, wadanda yawancinsu ke tsugune a makwabta sun yi kira ga gwamnatin jihar ta Anambra da ta gina hanyoyi da lafiyayyun magudanan ruwa domin kawo karshen ambaliyar ruwan sama a yankinsu.