✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ambaliyar ruwa ta raba mutum 400,000 da muhallansu a Kogi

WHO ta bai wa jihar tallafin kayan kiwon lafiya don amfanin wadanda lamarin ya shafa.

Kwamishinan Lafiya na Jihar Kogi, Dokta Zakari Usman, ya ce ambaliyar ruwa ta lalata yankuna 514, sannan ta raba mutum 400,000 da muhallansu a jihar. 

Ya ce mutum 17 ne suka mutu a Kananan Hukumomin jihar tara da abin ya shafa a jihar.

Kwamishinan ya bayyana hakan ne a Lokoja, babban birnin jihar a ranar Litinin, yayin da yake karbar wasu kayayyakin jinya daga Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) don taimaka wa wadanda ambaliyar ta shafa a jihar.

Ya ce wadanda ambaliyar ruwan ta shafa na bukatar kulawar lafiya.

Ya yaba wa WHO bisa wannan karimcin da sauran abokan hulda da suka taimakawa jihar tun bayan barkewar ambaliyar.

“WHO ta kasance tare da mu duk tsawon wannan lokaci. Tun da ambaliyar ruwan ta barke babu wanda na fara kira sai WHO. “Da wannan karamcin, an karfafa mana gwiwa, kuma yanzu haka gwamnati ta himmatu wajen bayar da tallafi ga jama’a,” inji shi.

Kwamishinan ya bayyana cewa, duk da raguwar ambaliyan ruwan, jihar na fuskantar wasu matsaloli na kiwon lafiya, tare da fargabar cewa za a dade a cikin wannan hali.

A halin da ake ciki, Hukumar Lafiya ta Duniya ta ba da gudummawar kayan agajin gaggawa don taimakawa wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a Jihar Kogi.

Wakilin WHO, Walter Kazadi ne ya mika kayan talalfi a ranar Litinin ga ma’aikatar lafiya ta jihar a Lokoja, inda ya ce sun bayar da tallafin ne domin rage radadin ambaliyar ruwan ga wandanda abin ya shafa.

Wakilin na WHO wanda ya samu wakilcin Dokta Edwin Isiotu Edeh, mai ba da shawara kan harkokin kiwon lafiyar jama’a da muhalli na kungiyar, ya ce kungiyar ta yi matukar farin ciki da matakin da gwamnatin jihar ta dauka na rage cututtuka da ka iya tasowa a sanadin ambaliyar ruwan.

Kazadi ya bayyana cewa ana sa ran kowane kayan talalfin zai yi jinyar mutum 10,000, wanda mutum 900,000 da ambaliyar ruwa ta shafa a jihar za su amfana.

Kayayyakin da aka bayar sun hada da gidan sauro, man tsaftace hannu da sauransu.

Wakilin na WHO ya kuma yi kira ga jama’a da su tausaya tare da taimaka wa wadanda ambaliyar ta shafa a jihar da ma Najeriya baki daya.