✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ambaliyar ruwa ta yi ajalin mutum 10 a Zimbabwe

Ana fargabar wata mahaukaciyar guguwar da ake kira Batsirai na kan hanya.

Mutum 10 sun rasa rayukansu a Zimbabwe, bayan da ambaliyar ruwa ta yi awon gaba da su a kokarin keta wani gulbi da ke iyakar Mozambique.

Wannan ne karon farko da aka samu mace-mace a kasar tun bayan isowar mahaukaciyar guguwar a Kudancin Afirka, inda ta kashe sama da mutum 80.

Kazalika guguwar ta raba sama da mutum 100,000 da gidajensu a kasashen Malawi da Mozambique da Madagascar a dalilin ambaliya.

BBC ya ruwaito hukumomi a Zimbabwe na cewa mahaukaciyar guguwar mai hade da ruwan sama ta lalata gidaje da gonaki da gadoji har ma da makarantu.

Kazalika ana fargabar wata mahaukaciyar guguwar da ake kira Batsirai na kan hanya, kuma za ta isa Madagascar ranar Asabar.