✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ambaliyar ruwa ta yi ajalin mutum 5 a Yobe

Daraktan hukumar SEMA na jihar ya tabbatar da faruwar lamarin.

Rahotanni da ke fitowa daga Jihar Yobe sun tabbatar da mutuwar mutane biyar yayin da gawarwaki biyu suka bace sakamakon ambaliyar ruwan da ta auku a Karamar Hukumar Potiskum ta jihar.

Aminiya ta ruwaito cewa, ambaliyar ruwan ta auku a sassa da dama na garin Potiskum biyo bayan mamakon ruwan sama da aka tafka a daren Lahadi.

  1. Mamayar Taliban: Shugaban Afganistan ya ranta a na kare
  2. ‘Yan Boko Haram 190 sun sake mika wuya a Borno

Wani mazaunin yankin mai suna Hamza Maidede, ya ce gine-gine da yawa a kewayen al’ummomin Nahuta sun rushe tare kari a kan kadarori da dama da suka salwanata.

Maidede ya ce “A halin yanzu muna cikin bakin ciki saboda wani jariri a unguwar ya rasa ransa yayin da gini ya rufta a kansa.

“Muna addu’ar Allah ya kare mu baki daya sannan muna neman dauki daga gwamnati a dukkan matakai”.

Babban Sakataren Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar (SEMA), Dokta Mohammed Goje ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce a halin yanzu tawagar bincike da aikin ceto na SEMA suna Potiskum inda suke gudanar da bincike tare da taimaka wa al’umma a kokarin gano gawarwakin da suka bace.

Goje ya kara da cewa, ana ci gaba da aiwatar da wani shiri na sauya matsugunin mazauna yankuna da ke fuskantar barazanar ambaliyar ruwa a Damaturu kamar yadda gwamnan jihar ya umarta.

Aminiya ta yi kokarin neman karin bayani daga bakin babban jami’i na Karamar Hukumar Potiskum, Salisu Muktari ta wayar tarho, inda ya ce a tuntubi hukumomin da suka dace don samun cikakken bayani.