✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ambaliyar ruwa ta yi wa sansanin soji barna a Borno

’Yan gudun hijirar dai a halin yanzu na neman mazaunin da za su tsuguna karkashin yanayin tsaro.

Rahotanni sun bayyana cewa ambaliyar ruwan da ta rutsa da dakarun sojin Najeriya ta jefa su cikin halin ni-’yasu yayin da ta afka wa sansaninsu da ke garin Malam Fatori a Jihar Borno.

Matsalar ambaliyar ruwan ta kara dagula yanayin hamada da sojoji ke ciki a yayin da suke ci gaba da fafatawa da mayakan ISWAP da ke da sansanoni a yankin da ke kusa da Tafkin Chadi.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, sojojin da ke Malam Fatori na ci gaba da nuna jarumta ba dare ba rana wajen tinkarar hare-haren da ’yan ta’adda ke kaiwa da makamai iri-iri da suka hada da bama-bamai da gurneti da kuma manyan motocin masu dauke da bindigogin yaki.

Sai dai mazarci kan al’amuran da suka shafi ta’addanci kuma kwararren mai sharhi kan yaki da tayar da kayar baya a yankin Tafkin Chadi, Zagazola Makama, ya ce ambaliyar ruwan ta janyo wa sojojin koma baya wajen fatattakar ’yan ta’addan.

A cewar Zagazola, tun tsawon makonni da aka fuskanci ambaliyar ruwan, daruruwan mazauna yankin musamman ma ‘yan gudun hijira, suka shiga kokawa kan rashin samun matsuguni da abinci da sutura.

Ya ce ’yan gudun hijirar dai a halin yanzu na neman mazaunin da za su tsuguna karkashin yanayin  tsaro.

Galibin sassan garin na Malam Fatori ba a iya shigarsa saboda ambaliyar ruwan da ta mamaye akasarin yankin.

Malam Fatori wanda shi ne babbar gari a Karamar Hukumar Abadam ya yi makwabtaka da Kogin Komadougou da ke Jihar Yobe da kuma gabar Tafkin Chadi, sannan kuma ya yi iyaka da Kasar Chadi da Jamhuriyar Nijar.