✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ambaliyar ruwan bana ta fi yi wa Jigawa barna fiye da kowace jiha – Minista 

Ministar ta ce gwamnati na bincike don tallafa wa manoman da abun ya shafa

Gwamnatin Tarayya ta ce Jihar Jigawa ce ta fi kowace a Najeriya fuskantar adadin mutanen da suka mutu a sanadin ambaliyar ruwa a fadin kasar nan a 2022. 

Ministar Jinkai da Agajin Gaggawa, Hajiya Sadiya Umar Farouk, ce ta bayyana hakan a ranar Laraba, yayin taron manema labarai a Fadar Shugaban Kasa, a Abuja.

Ministar, wadda ta jajanta wa wadanda lamarin ya rutsa da su, ta ce Jihar Bayelsa ba ta cikin jihohi 10 na farko da aka fi samun yawan mace-mace a kasar nan sabanin yadda ake bayyanawa.

Bisa kididdigar da ma’aikatar ta fitar, adadin mace-macen da aka samu a kowace jiha, adadin mutanen da suka rasa matsugunansu, adadin wadanda suka jikkata, gidajen da suka lalace, gonakin da suka lalace duk an kididdige su.

Kididdigar da ma’aikatar ta fitar game da ambaliyar ruwa a ranar 24 ga watan Oktoba, ta ce adadin wadanda suka mutu a Jigawa su ne 91, Anambra 77 yayin da a Kogi mutum 471,991 ne ambaliyar ta shafa amma babu wanda ya mutu.

‘Yan Najeriya 3,219,780 ne abin ya shafa a fadin kasar, yayin da adadin wadanda suka rasa matsugunansu ya kai 1,427,370, sai adadin wadanda suka mutu ya kai 612.

Da aka tambaye ta game da irin taimakon da gwamnatin tarayya za ta bai wa Jihar Bayelsa, bayan da tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan ya tattauna da Buhari da mataimakinsa Osinbajo, ministar ta ce ma’aikatarta ta kai kayan agaji Bayelsa tare da hadin gwiwar sojin saman Najeriya.

Ta kuma ce iftila’in ambaliyar ruwa lamari ne da ya shafi kasa baki daya, inda ta kara da cewa ma’aikatarta na yin aiki gwargwadon karfinta.

“Bayelsa ba ta cikin jihohi 10 da suka sha fama da iftila’in ambaliyar ruwa, Jigawa ce a kan gaba.”

Ministar ta kuma sanar da ci gaba da tantance gonakida da suka lalace don tallafa wa manoman da abun ya shafa.