✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Amfani da kazantar dabbobi ba ya maganin ciwon ido’

Kwararre a fannin lafiyar idanu a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano ya gargadi ‘yan Najeriya

Wani kwararre a fannin lafiyar dio a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano, Dokta Ibrahim Yuguda ya gargadi ’yan Najeriya su amfami abubuwan da ba a tantance sahihancinsu ba wajen maganin ciwon ido.

Da yake jawabi yayin bikin Ranar Gani ta Duniya ta bana a Kano, likitan ya ce kuskure ne a rika amfani da sukari, gishiri, ruwa, fitsari ko kashin shanu a matsayin maganin ciwon ido.

Ya shawarci jama’a su rika zuwa gwaji tare da neman shawarar masana a matsayin hanya daya tilo ta magance larurorin ido.

Dakta Yuguda ya kuma ja hankali kan sayen magungunan digawa a ido daga shagunan sayar da magani barkatai, yana mai cewa hakan na iya kara ta’azzara matsalar.

“Abin da ya kamata shi ne su je wurin masana domin a duba lafiyar idanun tare da ba su shawarar da ta dace.

“A fadin duniya, akwai sama da mutane biliyan biyu da ke fama da matsalar idanu iri daban-daban wacce za ta iya kasancewa mai sauki ko kuma mai tsanani.

“Daga cikin wannan adadi, sama da mutum miliyan daya za a iya magance matsalarsu har su warke sarai”, inji likitan.

Daga nan sai ya shawarci mutane, musamman wadanda suka haura shekaru 40 su rika ziyartar likitan idanu domin duba su akalla sau daya a kowacce shekara, domin hakan zai iya kare su daga kamuwa da makanta.