✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amfani da gidan sauro ne babban maganin zazzabin cizon sauro – Masana

Ta lura cewa yanayin damina na haifar da yawan yaduwar sauro.

Wata kwararriyar likita a Kano, Dokta Fauziyya Ahmed ta ce yin amfani da gidan sauro ne babban maganin kamuwa da zazzabin cizon sauro.

Likitar, wacce ta bayyana hakan yayin hirarta da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a Kano ranar Litinin ta ce gidan sauron ya fi tasiri la’akari da yanayin muhallanmu da ke cike da kwatoci kusan a ko ina.

Ta kuma yi gargadi a kan yin amfani da magunguna ba tare da shawarar masana ba, inda ta shawarci jama’a su tara kudi su sayi gidajen sauron.

“Gwamnatocin Tarayya da na Jihohi suna matukar kokari wajen raba gidajen sauro a duk shekara, amma jama’ar Najeriya sun yi yawan da ba zai yuwu kowa a wadatar da shi ba.

“Saboda haka nake bayar da shawarar su rika sayen gidan sauron da kansu, tunda dai ya fi magani ko allurar zazzabin cizon sauron arha,” inji ta.

Ta lura cewa yanayin damina na haifar da yawan yaduwar sauron, musamman a yankunan da ruwa ke yawan kwanciya.

Daga nan sai tayi kira ga jama’a kan su tabbatar da tsaftar muhallinsu domin kare karuwar saurayen da ke haifar da zazzabin cizon sauro. (NAN).