Amfanin gwaiba wajen gyaran jiki | Aminiya

Amfanin gwaiba wajen gyaran jiki

Sau da yawa mutane ba su cika damuwa da cin gwaiba ba, hakan ya sa tana daya daga cikin ‘ya’yan itacen da ba a ba su muhimmanci, inda wadansu sun ce ba sa son gwaiba ne saboda yawan kananan kwallayen da ke cikinta. Shin ko kun san cewa gwaiba na da matukar inganci wajen gyaran jiki da gashi? To idan ba ku sani ba sai ku sani yanzu.
Gwaiba na mayar da fata tsohuwa zuwa yarinya; domin tana dauke da sinadaran bitamin A da B da kuma C. Wadannan sinadaran na taimakawa wajen magance kodewa da kuma jemewar fata, inda kullum za ta kasance mai laushi da damshi da kuma kyalli.
Gwaiba na kara abubuwa kamar haka:
kara hasken fata
Sinadaran da ke cikin gwaiba na kara hasken fata, suna taimakawa wajen kare fata daga kwayoyin cuta. Za a iya daka ganyen gwaiba sannan a rika wanke fuska da shi don a magance kurajen fuska, don kuma fata ta kara haske.
kara tsawon gashi:
A samu gwaiba nunanniya kamar biyu, sai a ci sau uku a rana. Yawan cin gwaiba na taimakawa wajen fitowar gashin kai. Kuma ga shi na daya daga cikin abubuwan da ke kara wa mace kyawu. Gwaiba na dauke da sinadarin folic acid wanda ke taimaka wa mata masu juna biyu. Yawan cin gwaiba na taimakawa wajen girman jairin da ke cikin mahaifiyarsa kafin haihuwa.