✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amincewa da kasafin kudin badi da wuri zai kawo saukin rayuwa?

Tun da aka kaddamar da Majalisar Dokoki ta Kasa a watan Yunin da ya gabata, shugabannin majalisun  biyu, Sanata Ahmad Ibrahin Lawan na Majalisar Dattawa…

Tun da aka kaddamar da Majalisar Dokoki ta Kasa a watan Yunin da ya gabata, shugabannin majalisun  biyu, Sanata Ahmad Ibrahin Lawan na Majalisar Dattawa da takwaransa na Majalisar Wakilai Mista Femi Gbajabiamila, suka yi ta nanata niyyarsu ta tabbatar da cewa muddin Bangaren Zartaswa na Gwamnatin Tarayya da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ke jagoranta, zai gabatar wa majalisun kasafin kudin badi (2020), a karshen watan Satumba ko a farkon watan Oktoba, to, majalisun biyu za su jajirce, su tabbatar da amincewa da kasafin kafin shigowar sabuwar shekarar, ta yadda kasar nan za ta koma tsarin baya na aiki da kasafin kudi a farkon watan Janairun kowace shekara ya kuma kare a karshen watan Disamban shekarar.

Tun da aka dawo mulkin dimokuradiyya a 1999, yau sama da shekara 20, wannan  ne karo na biyar da aka taba amincewa da kasafin kudin wata shekara kafin kamawarta.

Tsaikon kan fara ne daga bangarorin biyu, da farko Bangaren Zartarwa ya yi ta nuku-nuku, har daf da karewar shekara bai mika wa majalisun dokokin kasafin kudin ba. Su kuma suna karba sai su fara hutunsu na Kirsimeti da sabuwar shekara,  sai sun komo a sabuwar shekarar sannan su fara aikin tsefe kasafin kudin, aikin da kan dauke su wata hudu zuwa biyar, ko ma fi.

In ma Bangaren Dokokin sun kammala duba kasafin, sun mika wa Bangaren Zartarwa, shi ma sai ya tantance abin da kasafin kudin ya sake kunsa, don gudun  CUSHEN da dan Majalisar Wakilai ta 8, Alhaji Abdulmumini Jibrin Kofa daga Mazabar Kiru da Bebeji a Jihar Kano ya bankado a shekarar 2017, ya kuma zargi wadansu takwarorinsa tare da hadin bakin ma’aikatan gwamnati na yi duk shekara.

A irin wannan yanayi ne mai karatu sai ka ga an dauki wata biyar zuwa shida ko ma fi duk shekara kafin Shugaban Kasa ya sa hannu a kan kasafin kudin shekarar.

Hakan kuma ko ba a fada ba mai karatu zai san cewa jinkirin yana kawo tsaiko wajen gudananar da ayyukan Gwamnatin Tarayya, musamman na raya kasa da sukan iya tsayawa cik, har shekarar ta kare, kamar yadda aka rika gani musamman a majalisun dokoki na takwas a tsakanin shekarar 2015 zuwa 2019, lokacin da Sanata Bukola Saraki da Honarabul Yakubu Dogara suke shugabancin majalisun dokokin biyu, inda aka yi ta samun jan-in-ja da jan kafa da zargin juna a tsakanin bangarorin biyu, a kan gudanar da ayyukan yau da kullum, kuma kowa na cewa a kan tsarin mulkin kasar nan yake gudanarwa. A gefe daya kuma talakawa da ake rawa da bazarsu suke zama cikin kunci da talauci da sauran matsalolin rayuwa.

A duk lokacin da aka samu kiki-kaka daga wadansu ’yan siyasa (musamman na jam’iyyun adawa) da irinmu marubuta da masu sharhi a kan harkokin siyasar kasar nan (’yan gaza gani su kyale), sai mu yi ta surutu babu fahimtar juna a tsakanin bangarorin biyu da kiraye-kirayen sai ’yan kasa su kawo CANJI, ta hanyar zaben mafi yawan ’yan majalisun dokoki na kasa da Shugaban Kasa daga jam’iyya daya, ta yadda za a rika samun fahimtar juna don gudanar da ayyukan raya kasa da za su kawo ci gaban al’ummar kasa baki daya.

To, yanzu ga wannan tsari ya samu, ta yadda Bangaren Zartarwa da na Dokoki, suke aiki kafada-da-kafada, abin da zuwa yau ba wani kudiri ko daftarin doka ko neman sahalewa a kan wani abu da Bangaren Zartarwa ya mika wa Bangaren Dokoki da Bangaren Dokokin ya yi biris da shi, balle kuma a karshe, ya ki amincewa da shi kamar yadda aka rika gani a zamanin Majalisun Dokoki karo na takwas, duk da kasancewar majalisun biyu, Jam’iyyar APC, mai gwamnatin tsakiya ita ke da rinjaye a cikinsu.

Duk da haka, yanzu kuma irin wadancan mutane da na kira ’yan gaza-gani a sama, mun kuma yi ca a kan Majalisun Dokokin biyu, kan jajircewar da suka yi wajen yin aiki tare da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari kamar yadda suka alkawarta tun farko.

Samuwar wannan hadin kai na aiki tare tsakanin bangarorin biyu, har wasunmu, mun fara kiran Bangaren Dokoki da cewa sun zama tamkar ’YAN AMSHIN SHATA.

A nan tamabayata ga masu irin wancan ra’ayi, ita ce, fada suke so bangarorin biyu su ci gaba da yi ta yadda wadannan shekara uku da rabi da suka rage wa Shugaba Buhari za su kare ba tare da ya tsinana wa talakawa komai ba, musamman na jihohin Arewa da har yanzu ba su gani a kasa ba, kamar yadda takwarorinsu na jihohin Kudu suke ganin ayyukan raya kasa, tun da Buharin ya zo kan karagar mulkin kasar nan a shekarar 2015?

A ganina, tunda a wannan karo Bangaren Dokokin ya mika wuya dari bisa dari na yin aiki tare da Bangaren Zartarwar, to, sai mu zuba ido mu ga gudun Bangaren Zartarwar wajen gudanar da ayyukan raya kasar da ya yi alkawarin aiwatarwa  da a baya Bangaren Zartaswar ya yi ta kokawa cewa bai samun hadin kai daga Bangaren Dokoki ba. ’Yan kasa dai sun zuba ido su gani a kasa, wai an ce da KARE ANA BIKI A GIDANSU, kuma ai dimokuradiyya ake yi, da zarar ta bayyana hadin kan bangarorin biyu na a cuci talakawa ne, kowa zai ji, zai kuma gani, kuma masu magana za su yi.