✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Aminiya na neman ma’aikata

Za a rufe karbar takardun ranar 3 ga watan Dismba, 2021.

Aminiya na neman ma’aikata a bangaren Aikin Jarida na Zamani (Digital Journalism).

Idan kun lakanci aikin jarida da amfani da kafafen sada zumunta wajen yada labarai sannan kuna bibiyar abubuwan da ke faruwa yau da kullum, to wannan dama ce a gare ku.

Aikin ya kunshi bincike, zakulo labarai da tantance su, gami da bibiyar al’amura da fahimtar harkar yada labarai ta hanyar kafofin zamani.

Dole ne mutum ya kasance ya iya rubutun Hausa, kuma yana iya Ingilishi, ya san abin da masu karatun labaran Hausa suke so, sannan ya mallaki shaidar karatu ta akalla digirin farko ko HND.

Aikin kwantaragi ne a Abuja, ya kuma kunshi yada labarai ta intanet da kafofin sada zumunta.

Dama ce ga maza da mata; wadanda suke ganin sun cancanta daga ko’ina, sai su aiko da takardunsu ta aminiyasocial@dailytrust.com, a rubuta ’Yan Jaridar Zamani a wurin Subject. Za a rufe karbar takardun ranar 3 ga watan Dismba, 2021.