✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amir din Boko Haram ya mika wuya ga sojoji

Amir Rugu Rugu ya mika wuya ga sojoji tare da iyalansa.

Wani babban shugaba a kungiyar Boko Haram, wanda ake kira Amir Adamu Rugu rugu, tare da iyalansa sun mika wuya ga sojojin Najeriya a Jihar Borno.

Amir Rugu rugu wanda babban kwamandan kungiyar ne ya mika wuya ne ga sojojin rundunar Operation Hadin Kai a ranar Alhamis a yankin Gwoza.

Wani babban jami’in tsaro ya tababtar mana cewa Amir Adamu ya mika wuya ne tare da matansa uku da ’ya’yansa ga dakarun Runduna ta 26 a garin Gwoza.

Wani mazaunin garin Gwoza wanda ya ce kowa ya sunan dan Boko Haram din a yankin, ya ce, “Godiya ta tabba ga Allah, yau sanannen shugaban Boko Haram, Amir Adamu Rugu Rugu ya mika wuya a Gwoz. Karshen BH yazo insha Allah”.

Amir Adamu Rugu Rugu ya yi kaurin suna wurin kai munanan hare-hare a kan sojoji da mazauna yankunan Dutsen Mandara da Dajin Sambisa da kuma Gwoza.

Mika wuyan nasa za zuwa ne bayan wasu shugabanni da mayakan Boko Haram tare da iyalansu mutum 1,081 sun mika wuya sojoji a Jihar Borno, bayan rikicin cikin gida da ya dabaibaye kungiyar bayan mutuwar shugabanta Abubakar Shekau.

Hukumomin sojin Najeriya sun ce kwamnadoji da mayakan Boko Haram na tururwaur mika wuya sakamakon matsa wa maboyarsu da luguden wuta ta kasa da kuma jiragen yaki.

Sojojin sun kuma ce rikicin shugabanci da yunwa da rashin lafiya da rayuwar wahalar da mayakan kungiyar suke ciki suna daga cikin abubuwan da ke sa wasunsu barin kungiyar.