✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Amotekun ta sake kama matafiya ’yan Arewa 151 a Ondo

An kama su ne a cikin wata tireka

Kwana uku bayan rundunar tsaro ta Amotekun ta kama matafiya ’yan Arewa 147 a Jihar Oyo, ita ma takwararta ta Jihar Ondo ta yi irin wannan kamun na mutum 151.

An kama matafiyan ne a Akure, babban birnin jihar a ranar Juma’a a cikin wata motar tirela da ta taso daga Arewa zuwa Kudu maso Yammacin Najeriya.

Da yake tabbatar da kamen, Shugaban kungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti-Allah reshen jihar ya Ondo, Alhaji Bello Garba ya shaida wa Aminiya cewa, “Gaskiya ne a ranar Juma’a da safe jami’an Amotekun sun tsare wata motar tirela da aka yi bincike aka gano tana dauke da mutane 127 da buhunan shinkafa da wake da babura guda 10.

“Rundunar ta bayar da umarnin tsare mutanen da suka mallaki wadannan babura guda 10 ne saboda bincike ya tabbatar da baburan ba su da takardu.

“Amma an sallami sauran mutanen saboda ba a gano haramtattun abubuwa ko makamai a tare da su ba.

“Rundunar ce ta gayyace ni zuwa wajen binciken da na tsaya da kaina domin ganin an yi masu cikakkun takardu zuwa yammacin wannan rana da aka sallame su,” inji shi.

Da yake yi wa ’yan jarida cikakken bayani, Kwamandan Rundunar Amotekun ta Jihar Ondo, Akogun Adetunji Adeleye, ya ce sun tsare motar ce daga ci gaba da tafiyar domin yin cikakken bincike a kansu.

Ya kuma ce, “Mun gano motar tana dauke da mutum 151 da aka boye su a karkashin buhunan shinkafa da wake da babura guda takwas.

“Mutanen sun ce sun fito ne daga jihohin Kano da Jigawa da Katsina. Dukkansu maza ne sai mata uku da suka kasa yin cikakken bayanin yadda suka hadu wuri daya suka shigo wannan mota kuma ba su fadi ainihin abun da suka zo yi ba.

“Ka san duk matafiyi akwai nufinsa na inda zai je da abun da zai yi amma sai cewa suke yi za mu je Akure a nan Jihar Ondo da Osogbo a Jihar Osun ne.

“Wannan bai dace ba amma saboda ’yancin kasancewarsu ’yan kasar Najeriya muka kyale su domin babu wani haramtaccen abu ko makami da aka samu a tare da su.