Daily Trust Aminiya - Amsoshin tambayoyin da suka shafi motsa jiki
Subscribe

Amsoshin tambayoyin da suka shafi motsa jiki

Sana’ata aikin karfi, kamar tura baro, dako da sauransu. Shin irin wannan wahalar da nake sha ta aiki ta wadatar ba sai na motsa jiki ba ko kuwa?

Amsa: An samu sabanin ra’ayoyi game da wannan batu wato ko shin leburori ma suna bukatar motsa jiki na musamman duk da ayyukansu na yau-da-kullum ya jibanci motsa-jiki. Akasarin masana sun nuna cewa wannan motsa jiki na leburanci yakan wadatar domin wasu leburorin ma abin da suke konawa na abincin jiki yana fin abin da ake so a kona a rana, domin har ‘fatigue’ wato gajiya suke yawan samu ta yadda idan ba su samu mai tausa ba, (massage), ko wankan ruwan dumi, ciwon jikin yau yakan kai washegari. Sai dai wadansu suna ganin akwai irin leburancin da ya fi wani alfanu ga jiki. Misali mai tafiya a kafa ko yana tura wani abu ko ba ya turawa, ko mai keken da ke shiga kwararo-kwararo yana talla, sun fi wanda ke tsaye wuri guda yana aiki kamar mai aikin kwasar kasa da shebur. Kuma suka ce mai aikin karfi mabambanta irin taka; yana dako, yana tura baro, yana kuma wasu abubuwan irinsu, ya fi zama wanda ke motsa duka sassan jiki a lokaci guda.

Ina turo tambayoyi ba na ganinsu. Kafata ce idan ina tafiya sai in ga jijiyoyi sun firfito amma idan na zauna sai su bace. Shin ko wannan matsala ce?

Daga Khalil Muhammad

Amsa: Watakila an amsa irin tambayarka a ranar, ko a ’yan kwanaki kusa da tambayar. Ko kuma ba ka sa suna ba. Amsarka ita ce cewa a’a wannan ba matsala ba ce, su ma kansu jijiyoyin jinin sun fi son haka shi ya sa kake ganinsu.

Ni kuma idan ina motsa jiki sai in rika jin ciwon gefen ciki. Ko akwai matsala?

Daga Zubair Mu’azu

Amsa: Eh, wannan zai iya nuni da matsala. Ka je a caji lafiyarka tukuna a ga ko akwai wani abu, domin akwai wadanda ba a son su rika wasu nau’uka na motsa jiki.

Da gaske ne wanda ke da kiba idan yana motsa jiki, sai ya zo ya ragu, idan ya daina kibar za ta dawo?

Daga Babangida Gambo da SB Kaduna

Amsa: Eh, da gaske ne idan mutum yana motsa jiki ya zo ya bari cikin ’yan makonni zai fara ganin nauyinsa na dawowa na masu kiba. Ko nauyin mutum bai karu ba, zai rika dai jin jikinsa ba dadi ba kamar lokacin da yake motsa jiki. Shi motsa jiki ana so mutum ya dore ne da shi, ko yana rage nauyi, ko ba ya rage nauyi, in dai ba karuwa nauyin ke yi ba, akwai alfanu. Don haka ake so mutum ya dauki daidai wanda zai iya jurewa da dorewa a kansa.

Shin da gaske ne kwanciya bayan cin abinci kai-tsaye na iya kawo illa?

Daga Saminu Artillery

Amsa: Eh, da gaske ne ana so mutum ya ba da akalla awa biyu zuwa uku idan ya gama cin abinci kafin ya kwanta. Illolin da rashin jiran kan kawo sun hada da amai, tashin zuciya, kumburin ciki, kwarnafi, warin baki da sauran matsalolin cushewar ciki.

Mukan ga wadansu mutane suna yawo suna auna jini suna auna hawan jini da cututtuka kamar maleriya, suna tallar magani. Su wadannan likitoci ne? Kuma hukuma ta yarda da su?

Daga Musa GGC Kurna

Amsa: A’a sai yau na fara jin irin wannan. Zai yi wahala a ce likitoci ne domin hukumar kiyaye aikin likitanci ta haramta wa likitoci yin talla. Likitoci idan suna nasu aikin a wajen asibiti (abin da suke kira outreach) za ka ji ana sanarwa. Sai sun sanar da hukumomi sun karbi izini kafin ma a sanar da jama’a. Za su sa ranaku da lokaci kaza zuwa kaza, kuma sukan yi aiki a kyauta. Ko masu sayar da magani wato Pharmacists ba a yarda su rika talla a titi ba. Don haka da alamu mutanen bogi ne ka guje su. Ko ma ku hada su da hukumomi na kusa da ku (ko na gargajiya ko na zamani) domin a dauki mataki a kansu.

Shin akwai illa ne mutum ya ji ba ya da lafiya sai ya tafi kyamis. Ko daidai ne?

Daga Aminu Muhammad

Amsa: Idan zan tambaye ka kai ma shin idan ka ji motarka ta fara gardama wurin makanike kake tafiya ko wurin mai sayar da kayan motoci (spare parts)?

Kasancewa muna fama da rashin ruwan famfo sai muka koma amfani da na rijiya wajen wanka da wanki da girki. To wani lokaci idan an janyo ruwan akan ga wasu abubuwa kamar kwari. Shin amfani da ruwan haka nan ba wani abu ga lafiya?

Daga Maman Hafsa

Amsa: Eh, ai ko ruwan famfo ma a wasu garuruwan a wannan zamani ana ganin abubuwa ciki. Ruwan rijiyar burtsatse mai zurfi rufaffiya ne kawai za a gan shi tar. A kimiyance irin wadannan ruwa masu abubuwa a ciki za a iya wanki da wanka da su kamar yadda kika fada. Sai dai bai kamata a sha kai-tsaye ba sai an dafa, ke nan za a iya girki da shi, tunda girki na dafa ruwan sosai.

Karin haske game da gurbataccen ruwa

Ina so a ba ni dama in jawo hankalin mutane game da kariya daga cutar kwalara. A rika shan ruwa mai tsabta, a kuma rika wanke hannaye da sabulu kafin a ci abinci, musamman yara. Kuma a rika wanke kayan itace da na lambu sosai kafin a ci

Daga Umar Sarkin Yakin Dausayin Kauna

More Stories