✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Amurka na neman kwace alakar kasuwancin China a Afirka

Amurka da shugabannin Afirka suna gudanar da taron koli, domin samar da damarmakin kasuwanci da za su amfani nahiyoyin biyu. Shugabannin na gudanar da taron…

Amurka da shugabannin Afirka suna gudanar da taron koli, domin samar da damarmakin kasuwanci da za su amfani nahiyoyin biyu.

Shugabannin na gudanar da taron ne a birnin Washington D.C bayan raguwar alakar kasuwanci da zuba jari tsakanin nahiyoyin, bayan kishiyar Amurka, China,  ta yi kaka-gida wajen harkar kasuwanci da albarkatun Afirka.

Sai dai a duk da taron, batun haraji da tsarin zuba hannun jari na barazana ga yunkurin na cimma matsaya mai ma’ana a tsakin bangarorin.

Wata sanarwa da kamfanin zuba hannun jari na AZA ta fitar a Amurkan, ta ce idan har Amurkan na son maye gurbin China, sai an warware matsalolin.

“A zahiri, hulda tsakanin Amurka da Afirka zai bada damar kasuwanci ba tare da biyan haraji ba, bisa dokar Amurka ta ci gaban yankin Afirka da damarmaki (AGOA).

“Yayin da dokar za ta taimaka wajen habaka kasuwanci, Amurkan ta dakatar da shirin a kasahen Habasha, Guinea, Mali, da kuma Sudan ta Kudu.

“Kuma tana shirin cire Burkina Faso a ranar 1 ga watan Janairu”, in ji sanarwar a kamfanin AZA.

Bukatar Afirkan dai ba a wuce fadada tsarin AGOA zuwa kasashen da Amurka ta dakatar a baya ba da kuma morar tsarin fitar da kayayyakinsu zuwa Amurka musamman fannin biyan haraji, inda Amurkan ta fi fuskantar togaciya daga Afirkan.