✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amurka ta cire Najeriya daga jerin kasashen da ke tauye ’yancin yin addini

A watan Disambar 2020 ne dai Amurkan ta saka Najeriya a jerin kasashen.

Kasar Amurka ta ce ta cire Najeriya daga jerin kasashen da ta shafa wa bakin fenti kan rashin bayar da cikakken ’yancin yin addini.

Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Anthony Blinken ne ya bayyana hakan a wata sanarwa ranar Laraba.

Ya bayyana hakan ne gabanin ziyarar da aka shirya zai kawo Najeriya.

Ya kara da cewa a baya, Gwamnatin kasarsa ta shafa bakin fentin ga kasashen Rasha da China da kuma wasu kasashe guda takwas, wadanda ya ce kurarsu ta yi kuka wajen musguna wa mutane a ’yancinsu na yin addini.

Sanarwar ta ce, “Gwamnatinmu ta damu matuka wajen tabbatar da cewa kowanne dan Adam ya sami ’yancin yin addini ba tare da an takura masa ba.

“Akwai kasashe irin su China da Burma da Eritrea da Iran da DPRK da Pakistan da Rasha da Saudiyya da Tajikistan da kuma Turkmenistan a matsayin kasashen da muke da damuwa a kansu wajen take hakkokin yin addinai.

“Bugu da kari, kasashen  Algeria da Comoros da Cuba da kuma Nicaragua za mu ci gaba da sanya ido a kansu matuka saboda yadda suke tauye hakkin mutane.

“Daga karshe, muna sanya kungiyoyin Al-Shabab, Boko Haram, Hayat Tahrir al-Sham, ’yan Houthi, ISIS, ISIS a yankin Sahara, ISWAP, Jamaat Nasr al-Islam wal-Muslimin, da kuma Taliban a matsayin kungiyoyin da suke da babbar barazana.

A watan Disambar 2020 ne dai Amurkan ta saka Najeriya a jerin kasashen da suke tauye ’yancin yin addinin.