✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Sakamakwon Zaben Gwamnonin Najeriya Na 2023 (Alkaluma Daga:INEC)

Amurka ta harbo balan-balan din leken asirin China

Lamarin ya sake farfado da zaman dar-dar a tsakanin kasashen biyu.

Sojojin Amurka sun ce sun harbo wani babban balan-balan din kasar China na leken asiri a yankin gabar tekun Carolina.

Kwanaki biyu da suka gabata ne wani babban balan-balan da ke shawagi a sararin samaniyar Amurka ya haifar da cece-kuce a harkokin diflomasiyya, kuma ya janyo muhawara a shafukan sada zumunta.

Kasar China ta dage kan cewa jirgin balan-balan din na wani kamfani mai zaman kansa ne, da ake amfani da shi don tattara bayanan Yanayi, iska ce ta ja shi zuwa sararin samaniyar Amurka bisa kuskure saboda ba ya iya sarrafa kansa sosai.

Sai dai Amurka ta ce ba tare da kokwanto ba, balan-balan din na leken asirin kasar China ne.

Gano wannan jirgi ya sa Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Antony Blinken, soke ziyarar da zai kai kasar China a karshen mako da nufin kawar da tashe-tashen hankula da suka yi kamari a tsakanin kasashen.

Ma’aikatar Tsaron Amurka ta Pentagon, ta ce jirgin balan-balan din yana dauke da na’urori masu auna firikwensi da na’urorin sa ido, ya nuna alamun yana iya sarrafa kansa da inda yake nufa.

Wannan lamari dai ya sake farfado da zaman dar-dar a tsakanin kasashen biyu ’yan kwanaki gabanin ziyarar da Blinken zai kai birnin Beijing.

Jirgin ya yi ta zagaye a wasu yankuna masu muhimmanci na garin Montana, inda aka lullube makaman nukiliya, lamarin da ya sa sojoji suka dauki matakin hana ta tattara bayanan sirri.

Wani mai magana da yawun Pentagon, ya ce jirgin zai iya kasancewa a sararin samaniyar Amurka na ‘yan kwanaki’, ya kuma nuna rashin tabbas game da inda jirgin zai dosa, ko kuma idan Amurka za ta yi kokarin kwace shi ba tare da tashin hankali ba.

Kuma da yammacin ranar Juma’a, Ma’aikatar Tsaro ta Pentagon ta amince da rahotannin wani jirgin balan-balan na daban da ke shawagi a yankin Latin Amurka – wanda aka kiyasta cewa balan-balan din leken asiri ne na kasar China.