✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Amurka ta kama masu daukar nauyin ’yan awaren Kamaru

Sama da mutane dubu 6 ne suka rasa rayukansu sakamakon rikicin ‘yan awaren.

Amurka ta tuhumi wasu mutane uku bisa zargin su da daukar nauyin ’yan awaren da ke fada da gwamnatin Kamaru tare da neman kafa kasarsu ta Ambazonia.

Mutanen uku da ke da takardun zama ’yan Amurka amma tushensu ke Kamaru, an zarge su da tara kudin da ya kai Dala dubu 350 domin saya wa mayakan ’yan awaren makamai da kuma kera bama-bamai.

Kazalika ‘yan awaren sun yi amfani da wani bangare na wannan kudin wajen yin garkuwa da jama’a da suka hada da wani babban limamin cocin Katolika da wani basaraken gargajiya.

Ma’aikatar Shari’ar Amurka ta bayyana mutanen uku a matsayin Claude Chi mai shekaaru 40 da Francis Chenyi mai shekaru 49 da kuma Lah Nestor Langmi mai shekaru 46, yayin da aka kama su a ranar Litinin din nan a wata kasar waje.

Ma’aikatar Shari’ar ta ce, kowanne daga cikin mutanen uku, na rike da babban makami a kungiyar ta masu fafutukar kafa kasar Ambazionia.

Ma’aikatar Shari’ar ta kara da cewa, mutanen sun samar da kudaden ne domin sayen makaman kaddamar da farmaki kan jami’an gwamnatin Kamaru da jami’an tsaron kasar da kadarorin gwamnati, baya ga sace faraen hula domin karbar kudin fansa.

Sama da mutane dubu 6 ne suka rasa rayukansu sakamakon rikicin ‘yan awaren, sannan fiye da miliyan guda sun rasa muhallansu.