✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amurka ta kashe jagoran Al-Ka’ida Aiman Al-Zawahiri

Amurka ta kashe Al-Zawahiri da jirgi mara matuki bayan ya koma wurin iyalansa

Amurka ta sanar cewa sojojinta sun hallaka jagoran kungiyar Al-Ka’ida, Aiman Al-Zawahiri a wani hari a kasar Afghanistan.

Shugaban Kasar Amurka, Joe Biden ya ce an kashe Al-Zawahiri ne ta hanyar harin jirgi mara matuki.

“Yanzu an yi hukunci na adalci, an kawar da jagoran ’yan ta’addan daga doron kasa,” inji Biden, a lokacin da yake tabbatar da rahoton kashe Aiman Al-Zawahiri a ranar Litinin.

Jagoran na Al-Ka’ida yana daga cikin mutanen da gwamnatin Amurka ke zargi da kitsa harin ranar 11 ga Satumbar 2001, wanda ya yi wa kasar mummunar illa.

Biden ya ce kashe Al-Zawahiri zai “zai sanyaya zukatan” iyalan mutanen da harin 11 ga Satumbar 2001 ta shafa.

Al-Zawahiri mai shekara 71, shi ne jagoran Al-Ka’ida tun daga shekarar 2011 bayan an kashe wanda ya asasa kungiyar, Osama bin Laden, a kasar Pakistan.

Kawo yanzu dai kungiyar Al-Ka’ida ko gwamnatin Taliban da ke jagorantar kasar Afghanistan ba su ce komai ba gane da ikirarin na Mista Biden.

Yadda aka kashe jagoran Al-Ka’ida Aiman Al-Zawahiri

A karshen mako ne Amurka ta kai harin jirgi mara matuki amma ta ki fitar da bayanin sai ranar Litinin bayan ta samu tabbacin rasuwar Al-Zawahiri.

Biden ya ce harin ya yi “nasarar kuma bai taba fararen hula ba.”

A cewarsa, a makon da ya gabata ne ya ba da izinin kai harin a ranar Asabar.

Ya ce an hallaka jagoran kungiyar ta Al-Ka’ida ne bayan ya koma wurin iyalansa a birnin Kabul, babban birnin kasar Afghanistan.

Amma ya ce, “Babu wanda harin ya taba daga cikin iyalan.

“Duk inda mutum ya biye, sai Amurka ta kwakulo shi, ta kawar da shi,” inji Mista Biden.