✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amurka ta kashe jagoran IS a Somaliya

Harin ya yi sanadiyar mutuwar al-Sudani da wasu mayakan kungiyar 10.

Dakarun musamman na Amurka a Somaliya sun kashe shugaban kungiyar IS na yankin arewacin kasar a wani samame da suka kai.

Hukumomi a Somaliya na cewa, dakarun musamman na Amurka da ke kasar sun kashe wani jigon kungiyar IS a samamen da suka kai wani kogo da ke arewacin kasar.

Bilal al-Sudani ya kasance shugaban kungiyar a yankin, kana mai taka rawa ga fannin sadarwar kungiyar a cewar sakataren tsaron Amurka Lloyd Austin.

A cikin sanarwar da ya fitar, Austin ya ce, wannan mataki ne da ya sanya Amurka da kawayenta cikin karin kwanciyar hankali, kuma hakan wata alama ce ta tsayin daka wajen kare Amurkawa daga barazanar ’yan ta’adda.

Sanarwar ta kara da cewa, shugaba Joe Biden ne ya bayar da umurnin kai harin wanda ya yi sanadiyar mutuwar al-Sudani da wasu mayakan kungiyar 10.

Rahotanni na nuni da cewa babu fararen hula da aka kashe ko suka ji rauni yayin kaddamar da harin.