✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Amurka ta lallashi UAE ta sayi jiragen yaki masu layar zana a wurinta

Hadaddiyar Daular Larabawa ta yi barazanar fasa cinikin kan tsauraran sharuddan da Amuka ke nen sa masa

Gwamnatin Amurka ta ce a shirye take ta sayar wa Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) jiragen yaki masu layar zana samfurin F-35.

Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Antony Blinken, ya lallashi Daular Larabawar ce a ranar Laraba bayan ta yi barazanar fasa cinikin saboda tsauraran sharudan da ta ce Amurka na neman sanya mata.

Ya bayyana cewa, “A shirye muke mu ci gaba da cinikin… matukar har yanzu Larabawan na da sha’awar hakan”, a lokacin da ya ziyarci kasar Malaysia.

A ranar Talata ce UAE ta sanar da shirinta na fasa cinikin jiragen da kudinsu ya kai Dala biliyan 23 da Gwamnatin Shugaba Joe Biden.

Gwamnatin tsohon Shugaban Amurka Donald Trump ce ta yi wa Daular tayin sayen jiragen, a wani mataki da ake gani a matsayin tukwici bayan UAE ta amince ta yi hulda da kasar Isra’ila.

Jjiragen F-35 jirage ne masu layar zana da ake amfani da su wurin tara bayanan sirri da leken asiri da yakin gaba-da-gaba a sararin samaniya da kuma kai hare-hare a kan abokan gaba a mafakarsu.

Bayan zuwan Gwamantin Biden, ta shardanta cewa za ta rika sanya ido sosai a kan jiragen saboda alakar UAE da China — wadda Amurka ke zargin tana iya amfani da jiragen wajen yin leken asiri a Amurka — wadda ba sa ga majici da Amurka, matakin da ya sa kasar Larabawar neman fasa cinikin.

A lokacin Trump, ’yan majalisa daga jam’iyyar Democrat ta Mista Biden sun yi yunkurin hana cinikin bisa zargin UAE da shiga yakin da ake yi da mayakan Houthi na kasar Yemen da kuma taimakon madugun yakin kasar Libya, Janar Khalifa Haftar; Amma hakarsu ba ta cim-ma ruwa ba.

Duk da cewa Blinken ya ki bayyana sharuddan da kasarsa ta nemi gindayawa a kan jiragen ba, ya ce manufar Amurka ita ce kare karfin ikon Isra’ila a bangaren aikin soji a yankin Gulf da kuma Gabas ta Tsakiya.

“Muna son tabbatar da cewa an yi cikakken bita a kan duk wata fasahar da za a sayar ko bayar ga wata abokiyar hularmu a yankin,” inji shi.

A baya dai Isra’ila, wadda ita ce babbar kawar Amurka a yakin Gabas ta Tsakiya ta nuna rashin amincewarta da sayar wa kasashen Larabawa jiragen F-35 din, a yunkurinta na kare matsayinta a yankin.

Amma daga baya ta janye bayan UAE ta zama kasar Larabawa ta farko ta da amince da ita a matsayin halastacciyar kasar Yahudawa.