✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Amurka ta saki dan damben Najeriya da ta tsare

An saki dan wasan damben Najeriya, Israel Adesanya, bayan kama shi da zoben tagulla a cikin kayansa a New York.

An saki dan wasan damben Najeriya, Israel Adesanya, bayan kama shi da zoben tagulla a cikin kayansa a New York.

An kama tsohon zakaran danbem duniya ajin marasa nauyi ne, a filin jirgin saman John Kennedy da ke New York a ranar Alhamis bayan an tsare shi.

Zobban dagulla na hannun da ’yan dambe ke sawa domin fada haramun ne shiga jirgi da shi ko a cikin jakar hannu ta shiga jirgi, sai dai a cikin kaya.

A wata sanarwa da manajansa, Tim Simpson, ya fitar ya ce, an warware matsalar an kuma saki dan damben, yana kan hanyarsa na zuwa gida.

Manajan ya kuma ce, wani masoyin dan danben ne ya ba shi zabban a matsayin kyauta kan hanyarsa ta zuwa filin jirgin, bai san cewa sa shi a jakarsa ta hannu laifi ne ba.

A farkon makon nan ne Israel ya kara da Alex Perera a wani wasan damben kare lambu na duniya ajin marasa nauyi, a inda Israel ya sha kashi a hannu wancan.