✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amurka ta tabbatar da yi mata kutse a shafukan intanet

Gwamnatin Amurka ta ce an yi wa shafukan tan a intanet na akalla hukumomi biyu kutse wanda ta ke zargin masu kutsen gwamnatin Rasha

Gwamnatin Amurka ta ce an yi wa shafukan intanet na akalla hukumominta biyu kutse wanda take zargin masu kutsen gwamnatin Rasha da kitsawa.

Kakakin Sashen Kula da Tsaron Intanet na Kasar (CISA) ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa, “Muna yin aiki tukuru da sauran abokan aikinmu wajen ganin mun magance tare da kwato shafukanmu na gwamnati da aka yi wa kutse.

“Sashenmu zai yi duk mai yiwuwa wajen ganin an takaita illar da harin zai iya yi mana.”

Jaridar Washington Post ta Amurka ta ruwaito cewa kutsen na da alaka da wanda aka kai wa kanfanin FireEye wanda ya ce maharan sun sace kayayyaki da dama da yake amfani da su wajen adana bayanan abokan huldarsa.

Kafafen watsa labarai a Amurka sun ce hukumar tsaro ta FBI ta fara binciken wasu mutane da ke aiki da Sashen Tattara Bayanan Sirri Wajen Rasha (SVR) wanda suka jima suna kwasar bayanan.

Ana kuma mutanen da yin kutse a shafukan wasu hukumomin gwamnatin kasar a zamanin mulkin Shugaba Obama.

“Gwamnatin Amurka na sane da duk wadannan rahotannin kuma za mu dauki dukkannin matakan da suka kamata wajen ganowa tare da magance wannan lamarin,” inji kakakin Majalisar Tsaro ta Amurka, John Ullyot.

Sai dai Ofishin Jakadancin Rasha a Amurka ya nesanta kasarsa daga harin tare da yin watsi da zargin inda ya ce ba shi da tsushe ballantana makama.

“Yin kutse a shafukan ko bayanan wasu kasashe ya saba da manufofinmu na hulda da kasashen waje da kuma dangantakarmu da kasashe,” inji sanarwar da ofishin ya fitar.