✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amurka ta yi amai ta lashe kan rikicin Chana da Taiwan

Ya ce za su tallafa mata da dakarun yaki

Shugaban Amurka, Joe Bide, ya lashe aman da ya yi cewa Amurka ba za ta tsoma baki a siyasar tsibirin Taiwan ba, inda a yanzu ya ce za su yi duk mai yiwuwa don ganin China ba ta mamaye yankin ba.

A wata hirarsa da wani gidan talabijin na Amurkan, Biden ya ce da zarar Chinan ta yi yunkurin kai hari Taiwan, kasar za ta dafa mata da rundunar tsaro.

Wannan yunkuri na Amurkan ga Taiwan, ya sha banbam da wanda ta yi wa Ukraine, domin ta tallafa mata ne da makamai ba rundunar yaki ba.

Wadannan kalamai na Biden dai sun jefa shakku a zukatan mutane, musamman bisa cin karo da dokar kasar ta 1979, da ta ce kasar ba za ta taimaka wa Taiwan din kai tsaye ba yayin rikici, ko ta ba ta dakarun yaki.

To sai dai Fadar Shugaban ta ce wannan doka fa tana nan daram, babu wani karan tsaye da aka yi mata.

Kasancewar ba goyon bayan ballewar tsibirin daga China suke yi ba, illa kare ta daga mamaya.